Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Asibiti, Sun Yi Awon Gaba da Ƙwararren Likita a Najeriya
- Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a wani asibitin kuɗi, sun yi awon gaba da ƙwararren likita a jihar Delta
- An ruwaito cewa maharan sun shiga asibitin a daren ranar Talata, suka tafi da likitan wanda ke shirin tafiya gida
- Wata majiya ta ce tuni aka sanar da ƴan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace na ceto likitan cikin ƙoshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani kwararren likita, Dr. Donatus Nwasor a kauyen Utagba-Uno, ƙaramar hukumar Ndokwa ta Yamma a Delta.
Maharan sun kutsa cikin asibitin likitan na kudi, suka yi awon gaba da shi da misalin ƙarfe 8:15 na daren ranar Talata.
Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya bayananta, ta shaidawa Punch cewa ɗaya daga cikin malaman asibitin da lamarin ya faru a gabanta ce ta sanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka sace likita
Ta ce likitan ya haɗa kayansa da nufin barin Asibitin da misalin karfe 8:00 na dare, kwatsam maharan suka farmake shi, suka tafi da shi zuwa wurin da ba a sani ba.
A rahoton Daily Post, majiyar ta ce:
"Malamar asibitin ta ce mai gidanta ya tashi da karfe 8:00 na dare, har ya shiga mota sai aka kira shi a waya, ya fito da nufin ɗaga kiran, kwatsam maharan suka shigo.
"Ƴan bindiga biyar ne suka fito daga daji, suka danne likitan suka tura shi cikin motarsa, sannan suka tafi. Ɗaya daga cikin masu garkuwan ya bar takalminsa ɗaya."
Wani bincike da al’ummar yankin suka yi ya nuna cewa daga baya an gano motar likitan a yashe a kusa da mahaɗar Iselegu da ke kan babbar hanyar zuwa Asaba.
Wane mataki aka ɗauka kan lamarin?
Majiyar ta bayyana cewa an sanar da iyalan Nwasor da duk wadanda ya kamata, kuma tuni aka kai rahoton lamarin ga ‘yan sandan a caji ofis na Kwale.
Lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Delta, Bright Edafe, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba har yanzu.
Ƴan bindiga sun sace jami'in NDLEA
A wani labarin, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Delta, sun sace wani babban jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA.
Ƴan bindigan sun sace jami'in ne a kusa da ofishin hukumar a daren ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng