Abba Ya Roki Sanusi II da Sauran Sarakunan Kano Alfarma a kan Tsare Tsarensa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya game da tsare-tsaren gwmantinsa
- Gwamnan ya bukaci goyon baya daga sarakunan gargajiya duba da yadda suke kusa da al'umma wurin wayar musu da kai
- Hakan na zuwa ne yayin da hadimin gwamnan a bangaren masarautu ya kai ziyara ta musamman a fadar Sarkin Rano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta nemi taimakon manyan masarautun gargajiya guda hudu da ake da su.
Gwamnatin ta nemi taimakonsu ne kan wayar da kan al'umma game da tsare-tsaren gwamnati da sauran shirye-shirye.
Gwamna Abba ya yi kira ga sarakunan Kano
Hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren masarautu, Farfesa Tijjani Naniya shi ya yi wannan kira ga masarautun jihar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Naniya ya bukaci taimakon masarautun ne yayin ziyara a fadar Sarkin Rano, Dr. Muhammad Umaru.
Ya bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya a cikin al'umma da gudunmawar da suke bayarwa.
Har ila yau, Naniya ya ce duba da yadda sarakunan gargajiya ke kusa da al'umma, sune ya fi dacewa su rika wayar da kan al'umma.
"Duk wani tsari ko shiri na gwamnati ya na samun cigaba ne idan ya samu goyon bayan sarakunan gargajiya."
- Farfesa Tijjani Naniya
Sarkin Rano ya ba da tabbacin kiran al'ummarsa
A martaninsa, Sarkin Rano, Dr. Muhammad Umaru ya yi godiya ga Naniya da mukarrabansa kan ziyarar.
Sarkin daga bisani ya tabbatar da cewa zai zage dantse wurin wayar da kan al'umma game da tsare-tsaren gwamnati.
Sanusi II ya nada dansa sarautar Chiroman Kano
Kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada babban dansa a matsayin Chiroman Kano a ranar Juma'a a fadarsa.
An nada DSP Aminu Lamido Sanusi ne a ranar Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki a fadar Sarki da ke Kofar Kudu.
Sarkin Kano ya tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da Magajin Garin Kano, Muhammad Nasiru Wada ya sanyawa hannu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng