Haɗarin Jirgin Ruwa Ya Ritsa da Shugaban Majalisa a Delta
- Ana cigaba da samun bayanai kan hadarin jirgin ruwa da aka yi a karamar hukumar Warri ta jihar Delta a ranar Talata
- Shugaban majalisar jihar Delta, Rt Hon. Emomotimi Guwor na cikin wadanda mummunan hadarin ya rutsa da su
- Emomotimi Guwor ya bukaci jami'an tsaro su yi bincike kan dalilin faruwar hadarin domin kiyaye faruwar haka a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Shugaban majalisar jihar Delta ya tsallake rijiya ta baya a wani mummunan haɗarin jirgin ruwa da aka yi a jihar.
Rt Hon. Emomotimi Guwor ya ce har yanzu bai gama farfaɗowa daga fargabar da ya shiga ba yayin hadarin.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa shugaban majalisar ya bukaci a yi bincike kan dalilin haɗarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hadarin jirgin ruwa a jihar Delta
A ranar Talata ne aka wayi gari da wani mummunan hadarin jirgin ruwa a karamar hukumar Warri ta Delta.
Lamarin ya jawo mutawar mutane biyar kuma har yanzu ana cigaba da neman rayukan da hadarin ya ritsa da su.
Shugaban majalisa ya tsallake rijiya da baya
Daily Post ta ruwaito cewa shugaban majalisar jihar Delta, Rt Hon. Emomotimi Guwor ya auna arziki kasancewar yana cikin waɗanda suka tsira yayin hadarin jirgin ruwa.
Emomotimi Guwor ya bayyana cewa ya shiga jirgin ruwan ne domin dawowa Asaba bayan ganawa da mutanen mazabarsa a ranar Juma'a.
"Kakakin majalisa ya shiga takaici matuka kan hadarin jirgin ruwan da ya faru a yankin karamar hukumar Warri.
Har yanzu bai fita daga fargabar abin da ya faru ba kuma yana yi wa iyalan wadanda suka rasu jaje.
Yana mika godiya ga Allah bisa ƙubutar da su da yi, yana yabawa jami'an tsaro kan agajin gaggawa da suka kawo musu.'
- Nkem Nwaeke, hadimin shugaban majalisar Delta
An yi hadarin jirgin ruwa a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu tarin yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane sama da 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Gummi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng