Halin kunci: Gwamna Ya Taimaka, Ya Ware Motoci domin Zirga Zirgar Mutane Kyauta

Halin kunci: Gwamna Ya Taimaka, Ya Ware Motoci domin Zirga Zirgar Mutane Kyauta

  • Gwamnatin jihar Edo ta samar da bas bas kyauta a fadin jihar domin yin zirga-zirgar al'ummarsa a kyauta
  • Gwamna Monday Okpebholo shi ya amince da hakan domin saukakawa al'umma duba da halin kunci da ake ciki
  • A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, matakin zai shafi dukan mazabun Tarayyan jihar da cikin birnin Benin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Monday Okpebholo ya zakulo hanyar saukakawa al'ummarsa a jihar Edo.

Mai girma Gwamna Okpebholo ya amince da daukar nauyin zirga-zirgar al'umma a cikin fadin jihar kyauta.

Gwamna ya ware bas bas domin zirga-zirgar mutane kyauta
Gwamna Monday Okpebholo ya samar da bas bas kyauta domin zirga-zirga a Edo. Hoto: Sen Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Gwamna ya ware bas kyauta domin zirga-zirga

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Fred Itua ya fitar a jiya Talata 26 ga watan Nuwambar 2024, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abba ya roki Sanusi II da sauran sarakunan Kano alfarma a kan tsare tsarensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Itua ya ce wannan na daga cikin himmatuwar gwamnatin Monday Okpebholo na inganta rayuwar al'ummarsa.

Sanarwar ta ce matakin zai shafi kewayen birnin Benin da kuma dukan mazabun Tarayya guda uku da ke fadin jihar, cewar Tribune.

Gwamnatin ta ce ta ware bas a ciki da wajen birnin Benin domin samun saukin zirga-zirga ba tare da kashe ko sisin kwabo ba.

Yankunan da za a yi zirga-zirgar kyauta

"An ware bas domin saukakawa al'umma, hakan zai ba mutane da ke shirin zirga-zirga cikin Benin da kewaye da dama ba tare da kashe ko sisin kwabo ba."
"Yankin Edo ta Tsakiya kamar su Ekpoma da Iruekpen da Irrua da Uromi da sauran wurare suna daga cikin bangaren da za a yi zirga-zirgar kyauta."
"Haka Edo ta Arewa kamar su Agbede sa Auchi da Okpella da Fugar da sauransu za su ci gajiya."

- Cewar sanarwar

Gwamna ya rushe masarautu a jihar Edo

Kara karanta wannan

Duba marasa lafiya kyauta ya tsokano bala'i, an kwantar da daruruwan mutane a asibiti

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Edo ta dauki wasu muhimman matakai kan sababbin masarautu da wata cibiyar al'adu.

Gwamna Monday Okpebholo shi ya dauki matakin inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II da martabarsa.

Wannan na zuwa ne bayan kirkirar sababbin masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta yi a zamaninta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.