"Da Rai na:" Obasanjo Ya Fito Ya Yi Magana, Ya Yi Mamakin Masu Yi Masa Fatan Mutuwa

"Da Rai na:" Obasanjo Ya Fito Ya Yi Magana, Ya Yi Mamakin Masu Yi Masa Fatan Mutuwa

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi tir da wadanda ke yi masa fatan mutuwa, yayin da aka fara yada labarin karya
  • Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a Osogbo, inda ya ce ya ga labarin da aka fitar ta shafukan sada zumunta da ke cewa ya mutu
  • Ya yi martani ga wadanda ke masa fatan komawa ga Mahaliccinsa, ya na mai cewa ba za su taba rabuwa da masifa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya musanta jita-jitar mutuwarsa da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Cif Olusegn Obasanjo ya ce yana nan da ransa tukunna, saboda haka bai dace a rika yada labarin kanzon kurege ba.

Kara karanta wannan

'Babu yadda za a yi shugabancin Najeriya ya dawo hannun mutanen Aewa," Okupe

Obasanjo
Obasanjo ya yi martani kan labarin mutuwarsa Hoto: Leigh Vogel
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito tsohon shugaban kasar, ya bayyana mamakin yadda wasu mutane za su yi masa irin wannan fata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun Obasanjo ya ce ya na nan lafiya

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Obasanjo ya gano akwai wasu da ke yi masa muguwar fata na mutuwa a kasar nan.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da titin Old Garage/Oke Fia-Lameco Dual Carriageway a Osogbo, Jihar Osun.

Obasanjo ya kwantar da hankalin iyalansa

Cif Olusegun Obasanjo ya ce tuni ya shaidawa iyalinsa cikin gaggawa cewa yana cikin ƙoshin lafiya bayan an samu rahoton mutuwarsa.

Ya ce:

“Na ji jita-jitar cewa na mutu. Na gani a kafafen sada zumunta. Na gaggauta sanar da ‘ya’yana da dangina cewa ba gaskiya ba ne, kuma ina nan da raye. Waɗanda suke son mutuwata, wannan shi ne fatan su.”

Tsohon shugaban ya yi fatan aniyar wadanda ke masa fatan mutuwa za ta koma kansu.

Kara karanta wannan

'Ku ja jari': Abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 ya ba matasa 25 kyautar N7.5m

Obasanjo ya magantu kan siyasarsa

A baya, mun ruwaito cewa tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce babu wata jam'iyyar siyasa da ya ke goyon baya a yanzu, duk da cewa a da shi dan PDP ne na tsawon shekaru.

Cif Obasanjo ya fadi haka ne a Abuja yayin bikin ranar haihuwar tsohon shugaban NDDC, Onyema Ugochukwu, inda ya bayyana ra'ayinsa kan siyasa da jam'iyyun da ake da su a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.