Tsohon Gwamnan Kogi Ya Musanta Zargin Almundahanar N110bn da EFCC ke Masa

Tsohon Gwamnan Kogi Ya Musanta Zargin Almundahanar N110bn da EFCC ke Masa

  • Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya musanta dukkanin zarge-zargen almundahana 16 da hukumar EFCC ke masa
  • Jami'an EFCC sun yi nasarar gurfanar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama bisa zargin wawashe N110bn
  • EFCC ta gurfanar da shi tare da wasu mutane biyu, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu, bisa badakalar da biliyoyin Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - A yau Laraba ne tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya musanta zargin da hukumar yaki da na masu kasa ta’annati (EFCC) ta yi masa a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban Mai shari’a Maryann Anenih a babbar kotun tarayya da ke Maitama.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban kotu a Abuja

Yahaya
Tsohon gwamnan Kogi ya musanta tuhumar almundahana da EFCC ke mas Hoto: @tboss_guy
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya musanta tuhume-tuhume guda 16 da EFCC ta yi masa a gaban alkaliyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da hukumar EFCC ke yi wa Yahaya Bello

Jaridar Punch ta wallafa cewa hukumar EFCC ta na zargin Yahaya Bello da handame kudin jihar Kogi har N110bn a lokacin da ya ke gwamna.

An gurfanar da shi tare da wasu mutane biyu, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu, bisa badakalar da ta yamutsa hazo.

EFCC ta zargi Yahaya Bello da kadarorin haram

Tuhumar da aka gabatar a gaban kotun da aka sanya wa lamba CR/7781, ta shafi haɗa baki, cin amana, da mallakar dukiya ta haramun.

EFCC ta zargi tsohon gwamnan da yin amfani da kudin jihar Kogi wajen siyan kadarori a sassa daban daban na babban birninta

EFCC ta gabatar da Yahaya Bello gaban kotu

A wani labarin kun ji cewa bayan an shafe tsawon lokaci ana wasan buya tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, an yi nasarar damke shi tare da kai shi kotu.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, jami'an EFCC sun kwamushe tsohon gwamnan jihar Kogi a Abuja

Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'adi ta dade ta na neman tsohon gwamnan, wanda ya sa EFCC ta ayyana neman shi a jallo bayan kin mutunta gayyatarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.