CBN Ya Shiga Damuwa kan Karancin Naira, Ya Shirya Wadata Bankuna da Kudi

CBN Ya Shiga Damuwa kan Karancin Naira, Ya Shirya Wadata Bankuna da Kudi

  • Babban bankin kasa (CBN) ya fara daukar matakin wadata 'yan Najeriya da takardar Naira duba da halin da ake ciki
  • A kwanakin nan, jama'a na kokawa da karancin takardun Naira daga bankuna da wasu daga cikin masu sana'ar POS
  • Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso ya tabbatar da cewa wannan karon, za a samar da kudin da zai wadaci jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babban bankin kasa (CBN) ya bayyana cewa an fara daukar matakin kawo karshen karancin takardar kudi a bankunan kasar nan.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya tabbatar wa bankuna samun wadataccen tsabar kudi don magance karancin Naira a fadin ƙasar.

Cardoso
Bankin CBN zai wadata bankuna da takardar kudi Hoto: @dipoaina1.
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Olayemi Cardoso, ya bayyana hakan ranar Talata a taron manema labarai bayan kammala taron kwamitin manufofin kuɗi (MPC) na 298 a Abuja.

Kara karanta wannan

TETFund ta gaji da kashe daloli, an dakatar da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN na kokarin kawo karshen karancin Naira

Olayemi Cardoso ya shaida cewa babban bankin CBN na tabbatar da cewa dukkanin bankunan ajiya na kuɗi suna samun wadataccen takardar Naira da ake buƙata.

Gwamnan CBN ya kara da cewa;

“Matakai da yawa muke ɗauka. Game da tsabar kuɗi, muna tabbatar da cewa duk bankunan ajiya na kuɗi suna samun duk tsabar kuɗin da suke buƙata,”

Bankin CBN ya binciki matsalar karancin kudi

Babban bankin kasar nan ya ce an gudanar da bincike kan dalilin karancin takardar kudi a kasar nan, kuma an gano abubuwa da dama.

Gwamnan bankin ya ce;

“Mun kuma gudanar da bincike kai tsaye a wasu wuraren, kuma abubuwa da dama sun fito daga waɗannan binciken, ba kuma za mu yi kasa a gwiwa wajen ɗaukar matakan ladabtarwa inda ya dace ba.”

CBN ya magantu kan amfani da tsohuwar Naira

A wani labarin, kun ji cewa babban bankin kasa (CBN), ya bayyana shirin janye amfani da tsohuwar takardar Naira, inda ake sa ran sababbin da aka buga za su maye gurbinsu.

Kara karanta wannan

Duba marasa lafiya kyauta ya tsokano bala'i, an kwantar da daruruwan mutane a asibiti

Tun a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne babban bankin ya fara shirin janye tsohuwar takardar Naira, sai dai an jinkirta daina amfani da kudin kai tsaye a lokacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.