An Kama Wanda Ya Damfari Miliyoyi da Sunan Malamin Musulunci, Sheikh Gadon Kaya
- Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wani mutum mai damfara da sunan shi dan uwan Abdallah Usman Gadon Kaya ne
- An ruwaito cewa mutumin yana bin shaguna yana karɓar kaya ne da sunan Sheikh, ya tura musu kudi ta asusun banki
- Bayan kama mutumin, yan kasuwa kimanin mutum 20 ne suka bayyana a gaban yan sanda da korafin cewa ya damfare su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - An kama wani mutum da ake zargi yana amfani da kama da yake da Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya yana damfara.
Mutumin mai suna Aminu Abdullahi dan shekaru 50 yana zaune ne a Kofar Nassarawa a jihar Kano.
Kakakin yan sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa mutumin ba shi da alaka da Sheikh Abdallah Gadon Kaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama ɗan damfara da sunan Sheikh Gadon Kaya
PM News ta wallafa cewa yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 50, Aminu Abdullahi da ake zargi da damfara a Kano.
Aminu Abdullahi yana zuwa shaguna yana cewa shi ɗan uwa ne ga Sheikh Gadon Kaya, idan ka amince da shi sai ya yi zamba.
Yadda asirin dan damfarar ya tonu a Kano
Wata rana Aminu Abdullahi ya je wani shago a Gwale ya karbi taliya ta N35,000 da sunan ya tura kudi ta asusun banki.
Da ba a ga shigar kudin ba, sai ya ce shi dan uwan Sheikh Gadon Kaya ne kuma saboda kama da suke da malamin aka amince masa ya tafi.
Tun bayan tafiyarsa kudin suka gaza shigowa wanda daga nan labarin ya tafi wajen yan sanda kuma aka kamo shi.
Aminu ya yi damfarar miliyoyin kudi
Bayan yan sanda sun kama Aminu, kimanin yan kasuwa 20 ne suka bayyana cewa mutumin ya sha zuwa ya damfare su.
A zuwa yanzu, an lissafa cewa Aminu Abdullahi ya damfari mutane kayan da kudinsu ya kai Naira miliyan biyu.
An kama babban dan daba a Kano
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wani kasurgumin dan daba.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Auwal ɗan daba ne bayan jami'an yan sanda sun dauki tsawon lokaci suna nemansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng