TETFUND Ta Gaji da Kashe Daloli, An Dakatar da Tallafin Karatu zuwa Ƙasashen Waje
- Hukumar ba da tallafin karatu ga manyan makarantu (TETFund) ta dakatar da daukar nauyin samun horo a kasashen waje
- An ji cewa hukumar ta ce matakin zai fara aiki a watan Janairu, 2025 duba da tsadar da karo ilimi ke da shi a kasashen ketare
- TETFund ta kuma bayyana yadda za ta rika bayar da tallafi domin samun kwarewa a wasu daga cikin makarantun Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Hukumar bayar da tallafin karatu ga manyan makarantu (TETFund) ta dakatar da tallafin karatu zuwa kasashen waje da ake ba makarantun gaba da sakandare.
Wannan na kunshe a cikin wata wasika da hukumar ta aika shugabannin jami'o'i da na kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi.
AbdulRazaq Ibrahim Fagge ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa wasikar mai dauke da sa hannun shugaban hukumar, Arc. Sommy S.T. Echono, an lissafa dalilan dakatar da tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan TETFUND na dakatar da tallafin karatun waje
Hukumar TETFund ta bayyana wasu manyan dalilai biyu da su ka tilasta mata daukar matakin dakatar da tallafin karatu zuwa kasashen waje. A wasikar da Legit ta gani, TETFund ta koka da tsadar karo kwarewa a ketare da kuma yadda wasu daga cikin malaman ke kin dawowa gida bayan sun fita.
TETFUND za ta ba da tallafi a makarantun Najeriya
Hukumar da ke bayar da tallafin ilimi ta kasa ta ce daga yanzu za ta rika daukar nauyin karo horo a jami'o'in da ke cikin Najeriya bisa wasu dalilai.
TETFund na ganin hakan zai kara bunkasa harkokin ilimi a cikin gida tare da rage bukatar neman Dala da ake yawan samu ga masu fita kasashen ketare.
ICPC ta kama daraktan TETFUND
A wani labarin, kun ji cewa jami'an hukumar yaki da rashawa ta ICPC sun cafke daraktan kudi da kula da asusun hukumar bayar da tallafin karatu ga manyan makarantu (TETFund).
An damke Misis Gloria Olotu bisa zargin cewa tana da hannu dumu-dumu a cikin wata badakalar kwangila N3.8bn da TETFund ta bayar, amma babu alamun an gudanar da aikin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng