Gwamnan Kano Ya Cika Alkawari, Ma'aikata Sun Fara Cin Sabon Albashin N71,000
- Gwamnatin Kano ta cika alkawarin da Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na fara biyan sabon mafi karancin albashin N71,000
- Shugaban ma'aikatan Kano, Alhaji Abdullahi Musa ya tabbatar da fara biyan sabon albashin a watan Nuwamba, 2024
- Ya roki ma'aikata su yi amfani da karin albashin wajen sauke nauyin da ke kansu cikin amana da tsoron Allah SWT
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N71,000.
Wannan dai na zuwa makonni uku bayan Gwamna Abba ya karɓa kuma ya amince da rahoton kwamitin albashi da ya kafa.
Gwamnan Kano ya fara biyan allbashin N71,000
Kamar yadda ta saba bisa al'ada, gwamnatin Kano ta biya kowane ma'aikaci albashin watan Nuwamba tare da ƙarin da ya kamata a ranar 25 ga wata, in ji Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, shugaban ma’aikatan Kano, Alhaji Abdullahi Musa, ya fara da godiya ga Allah maɗaukakin sarki.
Ya kuma yabawa mai girma gwamna bisa cika alƙawarin da ya yi na fara aiwatar da sabuwar dokar mafi karancin albashi.
Ma'aikata sun fara ganin sabon albashi a Kano
Shugaban ma'aikatan ya ce:
"Tun ranar da mai girma gwamna ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashin nan, na san cewa za a gani a aikace. Wannan karin albashin wata allura ce da aka wa ma'aikata, mu kara tashi tsaye.
"Mu tashi mu yi aiki tuƙuru kuma mu ji tsoron Allah a duk ayyukan da za mu yi domin mu ci halal."
Gwamnatin Kano ta fara biyan malaman lafiya
Alhaji Abudllahi ya ja hankalin ma'aikatan su yi amfanin da ƙarin kudin da suka samu ta hanyar da ta dace, su guji almubazzaranci.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta fara biyan alawus-alawus ga ma’aikatan lafiya a wani bangare na inganta jin dadin ma’aikata.
Abba Kabir zai kara tura talakawa karatu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara kara shirin tura ƴaƴan talakawa karatu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti mai dauke da mutane 18 da zai tantance daliban da za a zaba kafin a tura su karatun manyan digiri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng