Ana Shirin Kawo Tsarin da Zai Iya Sa a Dawo Karatun Boko da Hausa a Arewa
- Majalisar wakilai ta fara wani yunkurin kawo sauyi a kan harshen da ake amfani wajen isar da sako yayin karatun Boko a Najeriya
- Yan majalisa sun bukaci ma'aikatar ilimi ta duba yiwuwar amfani da harshen mutane wajen karatu da kuma alfanun da hakan zai haifar
- Lamarin ya biyo bayan wani kudirin da dan majalisar tarayya daga Legas, Hon. Kalejaiye Adebayo Paul ya gabatar ne a majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci ma'aikatar ilimi ta kasa ta duba yiwuwar sauya harshen da ake amfani wajen yin karatu a makarantu.
Majalisar ta ce ajiye harshen Turanci da rungumar harshen al'umma zai taimaka wajen bunkasa ilimi a Najeriya.
Jaridar the Nation ta wallafa cewa Hon. Kalejaiye Adebayo Paul ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bukaci sauya harshen karatu a makarantu
Majalisar wakilai ta dauko wani shiri da idan ya tabbata zai sauya tsarin karatun Boko a Najeriya.
Idan tsarin ya samu karɓuwa za a dawo anfani da harshen mutane a makarantu maimakon yaren Turanci.
Hakan na nufin cewa za a dawo amfani da yaren Hausa a mafi yawan jihohin Arewa idan kudirin ya tabbata.
Majalisar wakilai ta bayyana cewa za a bukaci amfani da harshen mutane ne a matakin karatun firamare da karamar sakandare.
A yanzu haka dai majalisar ta bukaci ma'aikatar ilimi ta kasa ta zabi wasu makarantu a Nijeriya domin jarraba tsarin.
Amfanin sauya harshe a makarantu
Hon. Kalejaiye Adebayo Paul ya bayyana cewa amfani da harshen mutane zai taimaka wajen bunkasa harkar ilimi da ilmantarwa a Najeriya.
Dan majalisar ya ce saboda amfani da Turanci da ake yi, Hausa, Yoruba da Ibo suna ƙoƙarin zama tarihi a makarantu.
Za a saka tsaro a makarantun boko
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ware N112bn a karkashin shirin samar da kudaden kula da tsaron makarantu.
Za a kashe kudin ne wajen tabbatar da cewa makarantu sun samu tsaro ga yaran da ke koyon karatu a shekaru uku masu zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng