Gyaran Matatu: Tinubu Ya Yabi Buhari, Za a Gyara Matatar da ke Arewacin Najeriya

Gyaran Matatu: Tinubu Ya Yabi Buhari, Za a Gyara Matatar da ke Arewacin Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna farin ciki kan fara aiki da matatar man Najeriya da ke Fatakwal ta yi a yau Talata
  • Bola Tinubu ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi matuƙar ƙoƙari wajen ganin matatun Najeriya sun dawo aiki
  • Haka zalika shugaba Tinubu ya bukaci NNPCL ya mayar da hankali wajen ganin matatun man Kaduna da Delta sun fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa kamfanin NNPCL kan gyara matatar man Fatakwal.

A yau Talata, 26 ga Nuwamba kamfanin NNPCL ya sanar da cewa matatar Fatakwal ta fara tace danyen mai.

Tinubu
Tinubu ya yi farin ciki da gyara matatar Fatakwal. Hoto: NNPCL|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Hadimin Bola Tinubu, Bayo Onanuga ne ya wallafa bayanan shugaban kasar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu da uwar gidarsa za su lula zuwa ƙasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi na'am da gyaran matatun mai

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar farin ciki kan ganin matatar man Najeriya ta Fatakwal ta fara aiki.

Bola Tinubu ya ce zai cigaba da ƙoƙarin kawar da kallon raini da ake yi wa Najeriya a matsayin ƙasa mai arzikin mai da ta gaza samar da matatu.

Tinubu ya yabi Buhari kan gyaran matatu

Bola Tinubu ya yabawa ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi a kan gyara matatun Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ce ta fara yunkurin farfaɗo da dukkan matatun man Najeriya.

Tinubu ya bukaci gyara matatar Kaduna

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa kamfanin NNPCL kan gyaran matatar Fatakwal.

Tinubu ya ce shugaban NNPCL, Mele Kyari ya yi kokarin kawar da duk wani ƙalubalen gyaran matatar Fatakwal.

Haka zalika Tinubu ya bukaci NNPCL ya gyara matatun man Kaduna, Delta da wata matar man kasar da ke Fatakwal.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi martani ga kalaman malamin addini kan sukar Tinubu

Shehu Sani ya yi magana kan farashin mai

A wani rahoton, kun ji cewa Shehu Sani ya bayyana jin dadi ganin yadda matatar Fatakwal ta fara tace danyen fetur kamar yadda ya dace.

Tsohon 'dan majalisar ya ce akwai bukatar shugaban kamfanin NNPCL ya waiwayi farashin mai a Najeriya domin saukakawa yan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng