Shugaba Bola Tinubu da Uwar Gidarsa Za Su Lula Zuwa Ƙasar Waje
- Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Faransa ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024 domin kai ziyarar aiki
- Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu zai tafi tare da mai ɗakinsa, Oluremi Tinubu domin amsa gayyatar shugaba Emmanuel Macron
- Bayo Onanuga ya ce Tinubu da Macron za su tattauna kan muhimnan batutuwa da suka shafi ƙasashen biyu domin inganta alaƙar da ke tsakani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai kama hanyar zuwa ƙasar Faransa daga birnin tarayya Abuja gobe Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024.
Shugaba Tinubu zai kai ziyara ƙasar ne bisa gayyatar shugaba Emmanuel Macron na ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai.
Hadimin shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwwa da ya wallafa a shafin X yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Bola Tinubi zai tafi Faransa a wata ziyarar aiki tare da uwar gidansa, Sanata Oluremi Tinubu da wasu manyan ƙusoshin gwamnatin Najeriya.
Abubuwan da Bola Tinubu zai yi a Faransa
Onanuga ya ce ziyarar ta kwanaki uku za ta mayar da hankali ne kan inganta dangantakar siyasa, tattalin arziki, da al’adu tsakanin ƙasashen biyu.
Haka nan kuma ya ce ziyarar Tinubu za ta duba hanyoyin samar da karin damammaki na hadin gwiwa musamman a fannin noma, tsaro, ilimi, da kiwon lafiya.
"Shugabannin biyu za su yi tarurrukan siyasa da na diflomasiyya inda zs su tattauna kan abubuwaɓ da suka shafi hada-hadar kudi, ma'adanai, kasuwanci da saka hannun jari.
"Sannan za su halarci taron kusuwanci tsakanin Najeriya da Faransa, wanda kamfanoni masu zaman kansu za sj halarta domin tattauna hanyoyin bunkasa t- attalin arziki.
- Bayo Onanuga.
Matar Tinubu za ta gana da uwar gidan Macron
A nata ɓangaren, matar shugaba Tinubu za ta gana uwar gidan shugaban ƙasar Faransa, Brigitte, inda za su tattauna kan tallafawa mata da kananan yara. da marasa galihu.
Bugu da ƙari, Tinubu da mai ɗakinsa za su halarci liyafar cin abinci da Macron zai shiya gabanin su dawo gida Najeriya.
Tinubu zai kawo karshen rikicin makiyaya
A wani rahoto, kun ji cewa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen jawo masu zuba jari a ɓangaren kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya.
Shugaban ƙasar ya faɗi hakan a wurin ratttaɓa hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin sarrafa nama a ƙasar Brazil.
Asali: Legit.ng