A Karshe, Jami'an EFCC Sun Ƙwamushe Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Abuja

A Karshe, Jami'an EFCC Sun Ƙwamushe Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Abuja

  • Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello bayan ya miƙa kansa a hedkwatarta da ke Abuja
  • Kakakin PDP na ƙasa, Dele Oyewale ya ce jami'an hukumar sun kama Yahaya Bello yau Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024
  • An ruqaito cewa tsohon gwamnan ya jagoranci tawagar lauyoyinsa zuwa ofishin EFCC domin kare kansa kan zargin karkatar da N80.2bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Yahaya Bello na tsare a hannun jami'an EFCC a hedkwatar hukumar ta ƙasa.

Yahaya Bello.
EFCC ta tsare Yahaya Bello a ofishinta da ke Abuja Hoto: EFCC, Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

EFCC ta kama tsohon gwamnan Kogi

Mai magana da yawun EFCC na ƙasa, Dele Oyewale ne ya tabbatar da kama tsohon gwamnan ga manema labarai ranar Talata, kamar yadda Leadership ta kawo.

Kara karanta wannan

Badakalar N110bn: Yahaya Bello ya tattaro tawagar lauyoyi, ya dura ofishin EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewale ya ce babban jami’in tsaro na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ne ya kama Bello yau 26 ga watan Nuwamba, 2024.

"Eh gaskiya ne, muna tsare da shi a hannun mu yanzu haka, dakarun hukumar EFCC ne suka cafke shi," in ji Oyewale.

Yahaya Bello ya amsa gayyatar EFCC a Abuja

Legit Hausa ta kawo maku rahoto a safiyar nan cewa Yahaya Bello ya je hedkwatar EFCC tare da tawagar lauyoyinsa domin amsa gayatar da aka masa.

Tsohon gwamnan ya dura ofishin EFCC da nufin kare kana kan zargin karkatar da kuɗaɗen da hukumar ke masa bayan tsawon lokaci yana ɓuya.

Idan ba ku manta ba a ranar 18 ga watan Afrilu, EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo kan zargin karkatar da Naira biliyan 80.2.

A halin yanzu, bayanai sun nuna cewa jami'an sashin bincike na EFCC na tsare da Yahaya Bello a hedkwatar hukumar da ke Jabi a Abuja.

Kara karanta wannan

EFCC ta taso tsohon gwamna a gaba, an fara binciken kwangilolin shekaru

Matasa sun ba Yahaya Bello shawara

A wani labarin, an ji cewa wata ƙungiyar matasa mai suna APC Youth Vanguard ta nuna damuwarta kan yadda Yahaya Bello ke ci gaba da ƙin kai kansa kotu.

Ƙungiyar ta nuna takaicin cewa rashin amsa sammacin kotu da tsohon gwamnan Kogi yake yi abin kunya ne ga jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262