Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu bayan Tinubu Ya Kore Ta

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu bayan Tinubu Ya Kore Ta

  • Tsohuwar ministar mata da walwalar jama'a, Uju Kennedy-Ohanenye ta koma kotu bayan korar ta da Bola Tinubu ya yi mata
  • A cikin wani bidiyo, ta bayyana lashi takobin yakar cin zarafi, musamman a shari’o’in da suka shafi ‘yan Najeriya da ke da rauni
  • Wakiltar wata yarinya ‘yar shekara biyar da aka ci zarafinta da tsohuwar ministar ta yi ya nuna jajircewarta na ganin an shimfida adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohuwar ministar harkokin mata da ci gaban jama’a, Uju Kennedy-Ohanenye, da Shugaba Bola Tinubu ya kora ta sake jan hankalin jama'a bayan komawarta kotu.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, Kennedy-Ohanenye ta nuna jajircewarta na ganin doka ya yiwa kowa adalci, musamman a shari'ar da ta shafi marasa galihu.

Ministar da Tinubu ya kora ta yi magana kan tsayawa marasa galihu a Najeria
Tsohuwar ministar Tinubu ta lashi takobin kwatarwa marasa galihu 'yancinsu a Najeriya. Hoto: @BarrUjuKennedy
Asali: Facebook

Jawabin da tsohuwar ministar ta yi

Kara karanta wannan

Duba marasa lafiya kyauta ya tsokano bala'i, an kwantar da daruruwan mutane a asibiti

A wani rubutu mai ratsa zuciya da tsohuwar ministar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina kan bakana na ganin an samu nagartacciyar al'umma. Har yanzu ban sauka daga turbar kwatarwa marasa galihu 'yancinsu ba a Najeriya.
"A yau, na wakilci wata yarinya 'yar shekara 5 da wani malamin ajinsu ya ci zarafinta. Lallai ba zan lamunci duk wani nau'in cin zarafi ba, musamman wanda ya shafi yara."

Uju Kennedy ta shirya tabbatar da gaskiya

A yayin da ta kara jaddada kudurinta na ganin an tabbatar da gaskiya da adalci ga wadanda aka yiwa ba daidai ba a kasar nan, tsohuwar ministar ta ce:

"Wannan shari'ar da na dauka a yau ta sake zaburar da ni wajen daure damarar yaki da masu cin zarafin yara da dangogin laifin.
"Ga wadanda ke tunanin aikata irin wannan laifi, to wannan sakon ya zama gargadi a gareku. Zan bi kadin duk wanda haka zalunta ba tare da sarewa ba."

Kara karanta wannan

'Ya manta asalinsa': Dan majalisar LP ya shan suka saboda sanya 'hular Tinubu'

Kalli bidiyon a kasa:

Shugaba Tinubu ya sallami ministoci biyar

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sallami mutane biyar daga majalisar ministocinsa, ciki har da ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye.

Bola Tinubu ya dauki wannan mataki ne bayan kiraye-kiraye da yan kasar ke yi masa na ya sallami wasu daga ministocinsa da suka gaza tabuka abin kirki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.