Badakalar N110bn: Yahaya Bello Ya Tattaro Tawagar Lauyoyi, Ya Dura Ofishin EFCC
- Yahaya Bello tare da rakiyar lauyoyinsa sun isa ofishin hukumar EFCC da ke Abuja a safiyar ranar Talata, 26 ga Nuwamba
- An ce tsohon gwamnan na Kogi ya tuka kansa zuwa ofishin EFCC domin amsa gayyatar da aka yi wa kan tuhume tuhumen rashawa
- Hukumar EFCC na tuhumar Yahaya Bello da karkatar da kimanin Naira biliyan 110 na kudin jihar Kogi a lokacin da yake mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya dura ofishin hukumar yaki da cin Hanci da rashawa ta EFCC kan zargin almundahana.
EFCC na bincike kan zargin da ake yi wa Yahaya Bello na karkatar da sama da Naira biliyan 100 na kudaden jihar Kogi a lokacin da yake mulki.
Yahaya Bello ya isa ofishin hukumar EFCC
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Yahaya Bello ya isa ofishin EFCC tare da tawagar lauyoyinsa a safiyar Talata, 26 ga watan Nuwamba 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa tsohon gwamnan ne ya tuka kansa zuwa ofishin EFCC a cikin wata mota kirar Hilux mai launin baki domin amsa gayyatar hukumar.
Wannan lamari ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli, wanda ya tabbatar da halaccin EFCC wajen gurfanar da Yahaya Bello ba a kotun jihar Kogi ba.
Yahaya Bello zai gurfana gaban kotu Laraba
A zaman baya, wanda Punch ta rahoto, EFCC ta nemi kotun da ta dage shari’ar saboda kwanakin da aka ba Yahaya Bello na amsa sammaci ba su cika ba.
Kotun ta ba da umarnin lika sanarwar gayyata a gidan Yahaya Bello da kuma wallafawa a jaridu domin tabbatar da bin doka.
A zaman kotun na karshe, an dage shari’ar zuwa 27 ga Nuwamba, 2024, inda a yau Talata aka ga Yahaya Bello ya je ofishin hukumar ta EFCC.
Yadda Yahaya Bello ya sake tserewa EFCC
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na ci gaba da yin wasan 'yar buya da jami'an hukumar EFCC kan zargin da ake yi masa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka ce EFCC ta gaza cafke Yahaya Bello a daren Laraba, 18 ga watan Satumbar 2028 bayan mamaye gidan gwamnatin Kogi da ke Asokoro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng