Gwamnatin Kaduna Ta Garkame Manyan Bankuna 3, Otal saboda Taurin Bashi
- Gwamnatin jihar Kaduna ta fara daukar mataki a kan kamfanoni da su ka bijrewa biyanta haraji kamar yadda doka ta tanada
- An rufe manyan ofisoshin kamfanoni 13 a jihar, a ciki har da fitattun bankuna da otal da wuraren cin abinci a sassan Kaduna
- Hukumar tattara haraji ta KADIRS ta samu sahalewar kotu bisa dokar tattara kudin shiga na jihar wajen daukar matakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta garkame wasu ofisoshin manyan bankuna da wuraren cin abinci da wasu kamfanoni.
Hukumar tattara haraji ta jihar (KADIRS) ce ta bayyana daukar matakin, inda ta ce kamfanonin da abin ya shafa sun hana gwamnati kudin haraji.
A sakon da KADIRS ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta rufe bankunan Unity, First Monument Bank, Zenith, Keystone, bisa hana gwamnati kudaden da su ka dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kaduna ta rufe kamfanoni
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar tattara haraji ta Kaduna ta rufe wasu kamfanoni da su ka hada da otal din Hamdala, Forte Oil da sauransu.
Gwamnatin ta yanke hukuncin aika ma'aikatanta domin garkame kamfanoni da dama a jihar, inda aka rufe ofisoshi akalla 13.
Dalilin rufe kamfanoni a jihar Kaduna
Hukumar KADIRS ta ce ta samu umarnin kotu don gaggauta rufe kadarorin gaba daya har sai an biya duk basussukan harajin amfani da ƙasa da ake binsu.
Gwamnatin Kaduna ta rufe kamfanonin ne bisa sahalewar sashe da 104 na dokar harajin kudin shiga ga jama’a da karamin sashe na 23 (1) (2) da (3) na dokar harajin jihar.
Gwamnan Kaduna ya magantu kan tsaro
A baya mun wallafa cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana wasu daga cikin hanyoyin da ya ke ganin zai dakile tasirin rashin tsaro da ke addabar Arewacin kasar nan.
Gwamna Uba Sani ya ce akwai bukatar gwamnonin da ke jagorancin jihohin shiyyar 19 su rika sanya matasa a cikin tsare-tsaren da su ka fitar na yaki da ta'addanci da rashin tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng