Gwamnatin Tinubu Ta Kammala Shirin Cefanar da Matatun Mai 4 Mallakin Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Kammala Shirin Cefanar da Matatun Mai 4 Mallakin Najeriya

  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da shirin gwamnati na sayar da matatun man fetur guda hudu da ake da su a kasar nan
  • Wannan mataki na zuwa a lokacin da matatar fetur da ke Fatakwal ta fara aikin tace danyen fetur domin tallafawa matatar Dangote
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Dare Sunday ne ya tabbatar da haka a sakon da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an kammala shirye-shiryen sayar da matatun mai huɗu mallakar gwamnati.

Ana shirin sayar da matatun man Fatakwal, Warri, Kaduna ga yan kasuwa a shirin gwamnatin tarayya na bunkasa tace danyen fetur.

Kara karanta wannan

'Ku ja jari': Abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 ya ba matasa 25 kyautar N7.5m

Tinubu
Za a cefanar da matatun kasar nan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Dare Sunday ne ya tabbatar da haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatun fetur 2 ne a Fatakwal

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an tattara manyan matatun kasar nan guda biyu a jihar Fatakwal, inda za su iya fitar da gangar fetur 210,000 a kullum.

Akwai karin matata guda a jihar Kaduna, kuma za ta iya tace ganga 110,000 a kullum, sai kuma wanda ta ke Warri, mai fitar da ganga 125,000 a kullum.

Dalilin gwamnati na cefanar da matatun fetur

A cewar Sunday Dare, gwamnatin Tinubu za ta cefanar da matatun ne domin taimakawa ta Dangote wajen tace fetur da yan kasa ke bukata.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa;

“Akwai shirin kammala sayar da matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna. Hakan zai ƙara wa masana’antar tace mai karfin aiki tare da taimakon matatun Dangote da na zamani da ake da su.

Kara karanta wannan

'Akwai yunwa': Tinubu ya magantu daga Brazil, ya ba yan kasa satar amsar shirinsa

Matatar Fatakwal ta fara aiki

A baya kun ji cewa matatar mai mallakin gwamnati da ke Fatakwal ta fara aikin tace danyen man fetur an shafe tsawon lokaci ana sanya ranar da za ta fara gudanar fitar da tataccen mai.

Babban jami'in sashen sadarwa na kamfanin mai na kasa (NNPCL), Femi Soneye ne ya tabbatar da hakan ga menama labarai, wanda hakan zai kawo karshen mita da ake yi na gazawar matatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.