'Najeriya Ta Gyaru a Lokacin Ku': Tambawul, PDP Sun Aika Sakonni ga Atiku
- Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya karbi sakonni daga PDP, Aminu Waziri Tambuwal da sauransu
- PDP da Tambawul sun taya Atiku murnar cika shekaru 78 a duniya tare da jinjina masa kan kokarin kawo ci gaba a Najeriya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kiraye kiraye ga 'dan siyasar da ya hakura da takarar shugaban kasa a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun aika sako ga Atiku Abubakar yayin da ya cika shekaru 78 da haihuwa.
PDP ta tuno yadda Atiku Abubakar ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin Najeriya a lokacin da yake shugaban majalisar tattalin arziki ta kasa.
Jam'iyyar PDP ta yabawa Atiku Abubakar
A wani sako da aka wallafa a shafin PDP na X, Hon. Debo Ologunagba, sakataren watsa labaran jam'iyyar ya yabawa Atiku kan rawar da ya taka wajen ci gaban Najeriya a 1999 zuwa 2007.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta nuna cewa majalisar NEC ƙarƙashin jagorancin Atiku, ta jawo tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka cikin sauri kuma ya zama mai ƙarfi.
PDP ta taya dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da yi masa addu'ar yin wasu shekarun a gaba.
Tambawul ya tuna da Atiku Abubakar
A nasa bangaren, Aminu Tambuwal ya yi murnar zataa ranar haihuwar Atiku Abubakar a madadin iyalinsa, yana mai yabon Atiku kan gudunmowarsa a ci gaban Najeriya.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Tambuwal ya yabawa Atiku kan karfafa dimokuradiyya da haɗin kan kasa, wanda a cewarsa ya daidaita lamura da dama a ƙasar.
Tambuwal ya kuma yaba da sadaukarwar Atiku wajen samar da hadin kan kasa, inganta sauye-sauyen tattalin arziki da inganta harkokin mulki.
'Ka hakura da takara' - Bode ga Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa Jigon PDP, Bode George ya bukaci Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa da ya hakura da takara a zaben 2027.
George, wanda tsohon mataimakin shugaban PDP ne ya ce shekaru sun ja da ya kamata Atiku ya koma gefe bayan shekaru 31 yana neman mulkin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng