EFCC Ta Taso Tsohon Gwamna a Gaba, An Fara Binciken Kwangilolin Shekaru

EFCC Ta Taso Tsohon Gwamna a Gaba, An Fara Binciken Kwangilolin Shekaru

  • Hukumar EFCC na binciken mu'amalolin kudi da kwangiloli da aka bayar a lokacin mulkin tsohon Gwamna Godwin Obaseki
  • Bayan sauka daga mulki, Obaseki ya ce ba ya tsoron bincike, yana mai cewa zai ba da hadin kai ga hukumar don fitar da gaskiya
  • Majiyar EFCC ta bayyana cewa hukumar ta sanya Obaseki cikin jerin wadanda take sawa ido domin gudun kada su terewa tuhuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta fara sanya ido kan dukkanin motsin tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, bayan kammala wa’adinsa a matsayin gwamna.

Obaseki, wanda ya bar ofis a ranar 12 ga Nuwamba, ya yi ikirarin cewa ya gamsu da ayyukan da ya yi a Edo kuma baya jin tsoron binciken EFCC.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya yi magana, kwanaki 10 da sauka an fara bincikensa

Hukumar EFCC ta sanya Obaseki a cikin jadawalin wadanda take bibiyar motsinsu
Obaseki ya shiga jadawalin wadanda EFCC ke bibiyar motsinsu. Hoto: @officialEFCC, @GovernorObaseki
Asali: Facebook

Hukumar EFCC na binciken gwamnatin Obaseki

Rahoton Punch ya nuna cewa EFCC ta kuma fara bincike kan kwangilolin da aka bayar a lokacin mulkin Obaseki na tsawon shekaru takwas a Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 2 ga Nuwamba, EFCC ta kama wasu jami’an gwamnati biyar da suka yi aiki a karkashin Obaseki, kan badakalar fitar kudi daga baitulmalin jihar.

Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa ana nazarin kwangiloli da hada-hadar kudi da aka gudanar a lokacin mulkinsa, domin gano ko akwai almundahana.

EFCC na sa ido kan motsin tsohon gwamna

Wasu majiyoyin EFCC sun ce binciken ya nuna cewa yawancin mu’amalolin kudi ko kwangila a mulkin Obaseki ba su da wata alaka ta kai tsaye da shi.

Wani jami’in ya bayyana cewa Obaseki da dukkanin tsofaffin gwamnoni suna cikin jadawalin wadanda EFCC ke bibiyar motsinsu domin hana su ficewa daga kasar.

EFCC ta ce ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa za a iya samun tsofaffin gwamnoni a duk lokacin da aka so yi masu tambayoyi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karbo bashin Naira tiriliyan 5.63 daga hannun ƴan kasuwa, ya yi ayyuka 2

'Ba na tsoron jami'an EFCC' - Obaseki

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bugi kirji da cewa ko kadan ba ya tsoron hukumar EFCC da binciken da za ta yi a kansa.

Godwin Obaseki ya ce a shirye yake ya mika wuya ga EFCC a duk lokacin da ta bukaci ganinsa domin ya san bai yi wani abin kunya a tsawon shekaru takwas na mulkinsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.