Majalisa Ta Fara Tuhumar Tinubu saboda Batun Karbo Aron Naira Tiriliyan 1.7
- Yan majalisun kasar nan sun bayyana mamakin yadda gwamnatin tarayya za ta bukaci karbo rancen makudan Daloli
- Wannan na zuwa bayan da gwamnati ta bayyana cewa ta samu damar tattara akalla $20bn bayan cire tallafin man fetur
- Sanata Adamu Aliero mai wakiltar PDP Kebbi ta Tsakiya ya ce akwai mamaki matuka ganin irin kudin da aka samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wasu daga cikin wakilan kasar nan sun yi tir da yunkurin gwamnatin Bola Tinubu na karbo sabon bashi.
Sanata Sani Musa da Hon Abiodun Falake sun bayyana ra’ayinsu ne yayin nazari kan daftarin kashe kudin gwamnati tsakanin 2025-2027.
Arise Television ta wallafa cewa shugaban Bola Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya karbo sabon bashin $2.2bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa na mamakin sabon rancen Tinubu
Jaridar Punch ta ruwaito cewa akwai mamaki matuka kan bukatar gwamnatin tarayya na neman sabon bashin bayan kudin da aka ce kasa ta samu.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ta samu tattara $20bn bayan cire tallafin man fetur.
Sanata Adamu Aliero mai wakiltar PDP Kebbi ta Tsakiya ya ce:
“Me gwamnati ta ke yi da kudin shiga daga ma’aikatun gwamnati da har ta ke neman sahalewar karbo bashi daga kasashen waje.?
Gwamnatin Tinubu ta yi martani ga majalisa
Shugaban hukumar tattara haraji (FIRS), Zacchaeus Adedeji ya bayyana cewa dama akwai bukatar karbo rancen a cikin kasafin kudin 2024.
Ya kara da cewa tun bayan da majalisa ta amince da kasafin kudin, ya yi daidai da ta yi amanna da gwamnati ta karbi rancen.
Majalisa za ta nazarci bukatar shugaba Tinubu
A baya mun wallafa cewa yan majalisar wakilai daga jam’iyyun adawa ka iya kawo cikas ga bukatar Bola Ahmed Tinubu na karbo sabon rance da ya kai N1.77trn domin cika kasafin kudi.
Wannan na zuwa bayan majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban, lamarin da wasu daga cikin yan jam’iyyar APC da ke a majalisar wakilai su ka sha alwashin marawa Tinubu baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng