'Ban Saka Shi ba': Gwamna Ya Fusata da Katobarar Hadiminsa, Ya Dakatar da Shi
- Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya fusata matuka da rubutun da daya daga cikin wani hadimansa ya yi
- Gwamnan ya dakatar da Mr Wale Ajetunmobi daga mukaminsa na musamman bayan wallafa bayanai marasa tushe
- Wannan na zuwa ne bayan dakataccen hadimin ya yi magana kan cafke waɗanda ake zargi a zanga-zangar EnSARS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya fatattaki hadiminsa a bangaren kafofin watsa labarai.
Gwamna Sanwo-Olu ya dakatar da Mr Wale Ajetunmobi saboda wallafa wasu bayanai a shafin X da ba su inganta ba.
Hadimin gwamnan Legas ya jawowa kansa dakatarwa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Gboyega Akosileya fitar a yau Talata 26 ga watan Nuwambar 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan wallafa rubutu da Ajetunmobi ya yi game da zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.
A rubutun, ya ce an cafke waɗanda ake zargi da kone-kone a zanga-zangar EndSARS kuma an hukunta su, Premium Times ta ruwaito.
Sai dai Legit Hausa ta yi bincike inda ta tabbatar a yanzu babu rubutun a shafin nasa na X da take zargin gogewa ya yi.
Gwamna Sanwo-Olu ya fadi matsayarsa kan bin ka'ida
A cikin sanarwar, Akosile ya ce gwamnatin Sanwo-Olu ba ta goyon bayan cin zarafi kuma ba za ta taɓa goyon bayan haka ba.
"Dakatarwar na zuwa ne bayan ya bayyana wasu bayanai marasa inganci a shafinsa na X."
"Gwamnatin Sanwo-Olu ba za ta taba goyon bayan cin zarafi ba kuma ta yi Allah wadai da hakan saboda ba haka muke ba kuma ba hanyar da muke bi ba ne."
- Gboyega Akosile
Hadimin Gwama Eno ya yi murabus
Kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya rasa hadiminsa na musanman da ya dade yana aiki a gidan gwamnatin jihar.
Hadiminsa a bangaren wayar da kan al'umma, Aniekeme Finbarr ya yi murabus daga mukaminsa domin neman sauya layi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin mutuwar matar gwamnan da ake shirin binne ta a cikin wannan mako da muke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng