'Sharrin Kwankwaso ne': Dan Majalisar NNPP Ya Yi Martani kan Shirin Tumbuke Shi
- Dan Majalisar Tarayya a NNPP daga jihar Kano, Hon. Ali Madaki ya magantu kan shirin tuge shi daga mataimakin shugaban marasa rinjaye
- Ali Madaki ya zargi Rabi'u Kwankwaso da shirya manakisar inda ya ce aikin banza suke yi saboda ba dan jam'iyyar ba ne
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu yan Majalisar daga NNPP suka shirya tube shi daga muƙamin nasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dokoki, Hon. Ali Madaki ya yi magana kan shirin tuge shi a muƙamin.
Madaki ya yi fatali da shirin tube shi da wasu yan Majalisar NNPP ke yi inda ya ce abin dariya ne.
Madaki ya soki Kwankwaso kan neman karya shi
Dan Majalisar ya zargi Rabi'u Kwankwaso da shirya manakisar inda ya ce ba su da wani ikon kan abin da suke shiryawa, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ali Madaki ya ce korarrun shugabannin jam'iyyar ba su isa su yi wani abu kan tsige shi a muƙamin nasa ba.
Ya koka kan yadda su ke cigaba da daukar Sanata Kwankwaso wani mai gida kamar bai yin laifi a rayuwarsa.
Madaki ya ce an kori Kwankwaso a NNPP
"Su wadanda suka sanya hannu a takardar ba yan jam'iyyar ba ne, da shugaban da mambobin gudanarwa duk kotu ta kore su a cikinta."
"Wannan kawai aikin banza suke yi, Kwankwaso ba dan jam'iyyar ba ne."
"Kun san cewa kullum zasu yi ta kokarin farantawa Rabiu Kwankwaso da bin duk abin da ya ce."
- Ali Madaki
Dan Majalisar ya ce ko kadan abin da suke shiryawa da duk wani makarkashiya bai dame shi ba.
Ya ce abu mafi dadi shi ne shugaban jam'iyyar NNPP, Dr. Boniface Aniebonam zai yi jawabi kan matsalar da ake ciki.
Dan Majalisar NNPP ya shiga matsala a Kano
Kun ji cewa yan NNPP a majalisar wakilai sun buƙaci cire Hon. Ali Madakin Gini daga matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Jam'iyyar NNPP ta ƙasa ta maye gurbinsa da Hon. Tijjani Jobe, mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng