Kwana Ya Kare: Manyan Malaman Jami'ar TSU 3 Sun Rasu Cikin Awanni 72 a Najeriya
- Malamai uku a jami'ar jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya sun riga mu gidan gaskiya cikin awanni 72
- Farfesa Akporido Samuel, Dr. Kiliobas Sha’a da kuma Dr. Ibrahim Saleh Bali sun rasu ne a tsakanin ranar Alhammis zuwa Lahadi
- Shugaban ASUU reshen jami'ar TSU ya kaɗu da rasuwar malaman, inda ya ce a yanzu suna rayuwa ne cikin ƙunci saboda tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Jami'ar jihar Taraba (TSU) da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta shiga jimami yayin da manyan malamanta uku suka rasu a cikin sa'o'i 72.
Farfesa Akporido Samuel, tsohon shugaban sashen kimiyyar sinadarai, ya riga mu gidan gaskiya a ofishinsa da ke cikin jami'a ranar Alhamis da ta gabata.
Dr. Kiliobas Sha’a, tsohon shugaban sashen Biological Science, da Dr. Ibrahim Saleh Bali sun rasu da safiyar ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda malamai 3 na jami'ar TSU suka rasu
An ruwaito cewa Farfesa Samuel ya fadi ya mutu a ofishinsa yayin da Dr. Kiliobas Sha’a ya rasu ne a gidansa bayan ya yi fama da cutar hawan jini.
Haka nan kuma na ukun, Dr. Ibrahim Bali ya rasu ne a asibitin FMC da ke Jalingo bayan fama da doguwar jinya.
Rasuwar lakcarorin cikin kwanaki uku ya jefa abokan aikinsu da sauran ma'aikatan jami'a cikin fargaba da alhini, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Malaman jami'ar sun jima suna rokon gwamnatin Taraba ta ƙara masu albashi kuma ta inganta walwalarsu amma har yanzu ba ta yi wani abin a zo a gani ba.
ASUU ta nuna damuwa kan lamarin
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen jami’ar jihar Taraba, Dr. Mbave Joshua, ya bayyana kaduwarsa da rasuwar malaman.
Ya kuma koka kan yanayin aiki da walwalar malaman jami'ar inda ya ce lakcarorin sun wayi gari cikin matsalar kudi saboda tsadar rayuwa da ake ciki.
Ciyaman ya yi mutuwar bazata a Legas
A wani labarin, kun ji cewa an shiga rudani a jihar Lagos bayan mutuwar bazata da shugaban karamar hukuma ya yi cikin wani irin yanayi.
Hakan ya faru ne bayan rasuwar shugaban karamar hukumar Onigbongbo, Oladotun Olakanle a ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
Asali: Legit.ng