Gwamna Radda Ya Gabatar da N682bn a Matsayin Kasafin 2025, An Lissafa Manyan Ayyuka

Gwamna Radda Ya Gabatar da N682bn a Matsayin Kasafin 2025, An Lissafa Manyan Ayyuka

  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya gabatarwa majalisar dokokin Katsina N682bn a matsayin kasafin kudin jihar na 2025
  • A kasafin na 2025, Radda ya ware N157.97bn domin ayyukan yau da kullum da kuma N524.27bn domin manyan ayyuka
  • A yayin da bangaren ilimi ya fi kowane bangare samun kaso, gwamnan ya warewa fannin tsaro kaso 3% na kasafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatarwa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2025.

Gwamna Dikko Radda ya gabatar da N682,244,449,513.87 a matsayin kasafin kudin jihar Katsina na shekarar 2025 mai zuwa.

Gwamnan jihar Katsina ya lissafa bangarorin da suka fi samun kaso a kasafin kudin 2025
Gwamnan Katsina ya gabatar da daftarin kasafin kudin jihar na 2025 ga majalisa. Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Tsohon mai ba Gwamna Radda shawara ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, Isah Miqdad ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce kasafin zai mayar da hankali ne musamman kan ilimi, samar da abinci ta hanyar bunkasa noma, samar da ayyukan yi, da kuma tsaro.

Kara karanta wannan

Sarki mafi daɗewa a sarauta, Muhammadu Inuwa ya rasu yana da shekaru 111

Yadda aka kasafta abin da Katsina za ta kashe

An ware N157.97bn (23.15%) domin ayyukan yau da kullum da kuma N524.27bn (76.85%) domin manyan ayyuka, wanda ke nuni da karin kashi 40% daga kasafin bara na N200.54bn.

Bangaren ilimi ne aka fi warewa kudi da N95.99bn (14%), sannan noma da kiwo su na biye da N81.84bn (12%).

Wasu bangarorin sun hada da ayyuka, gidaje, da sufuri (N9.68bn, 10%), ci gaban karkara da zamantakewa (N58.73bn, 9%) da albarkatun ruwa (N53.83bn, 8%).

Tsaro ne koma baya a kasafin jihar Katsina

Bangaren muhalli ya samu N49.84bn (7%), lafiyar jama’a ta samu N43.88bn (6%), yayin da tsaro aka ware masa mafi karanci, kashi 3% wanda ya kai N18.94bn.

Rahoton Ibrahima Kaulaha Mohammed, sakataren watsa labaran gwamnatin Katsina, ya ce an ware kashi 31% na kasafin da ya kai N230.76bn ga wasu bukatun jihar da ba a tantance ba.

Kara karanta wannan

Tattalin arzikin Najeriya ya fara farfadowa, NBS ta bayyana ci gaban da aka samu

Gwamna Radda ya bayyana gamsuwarsa da nasarorin da aka samu daga kasafin 2024, yana mai cewa an samu karin kudin shiga da ingantattun ayyuka.

Radda ya jinjinawa jami'an da suka mutu

Ya nuna cewa an rage matsalar ‘yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a yawancin kananan hukumomi, yana fatan kasafin 2025 zai kara bunkasa tattalin arziki.

Gwamnan ya godewa abokan hulda, ma’aikatan gwamnati, jami’an tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki, yana kuma jinjinawa jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Ya yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina da ta hanzarta amincewa da kasafin kudin 2025 don tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati akan lokaci.

Gwamna Inuwa ya gabatar da kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatarwa majalisar dokokin jihar da kasafin kudin 2025 na N320.11bn.

Kara karanta wannan

'Ku ja jari': Abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 ya ba matasa 25 kyautar N7.5m

An rahoto cewa Gwamna Inuwa ya warewa fannin noma kashi 3.9 kacal daga kasafin na badi, duk da cewa noma shi ne fannin da tattalin arzikin jihar ya dogara a kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.