An Harbe Ango a Ranar Daurin Aurensa, Amarya ta Gigice
- Kisan gilla da aka yi wa wani ango a yankin Kwale a karamar hukumar Ndokwa a Delta ya jefa al'umma a tashin hankali
- Wasu miyagu dauke da bindiga sun kai farmaki kan mutane, suka kashe wani ango a ranar Juma'a ana tsaka da shirin daurin aurensa
- Shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa an kashe angon ne yayin da yake tafiya sayayya tare da wasu abokansa a safiyar ranar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Wasu da ake zargi yan kungiyar asiri ne sun kashe ango ana shirin daura masa aure a jihar Delta.
Rahotanni sun nuna cewa bayan kisan angon, miyagun sun yi mummunan rauni ga wani mutum daya.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mutanen yankin sun shiga cikin fargaba saboda hare haren yan kungiyar asirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An harbe ango ranar daurin aure
Kwanan wani ango ya kare yayin da yan kungiyar asiri suka afka masa ana shirye shiryen daurin aurensa.
Lamarin ya sanya amarya da yan uwansa bakin ciki kasancewar ranar murna ta zamo ranar zaman makoki.
"Yana cikin tafiya tare da abokansa domin sayen wasu kayyakkin daurin aurensa, yan kungiyar asiri suka afka musu"
- Shaidar gani da ido
Yan sanda sun tsananta tsaro bayan harbe ango
Bayan kashe angon, an samu wata gawa da aka yasar a wani waje kuma yan kungiyar asirin sun jikkata wani mutum daya.
Daily Post ta ruwaito cewa rundunar yan sanda ta kara tsananta tsaro a yankin duk da cewa ba ta yi bayani a hukumance ba.
Halin da aka shiga bayan bindige angon
Mutanen yankin sun bayyana cewa suna cikin tashin hankali kasancewar yan ta'adda sun yawaita a yan kwanakin nan.
Al'ummar sun bukaci jami'an tsaro da su dauki matakin maganin yan ta'addar a kan cewa za su cigaba da kai hare hare saboda matsowar Kirsimeti da sabuwar shekara.
An fatattaki yan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta fatattaki wasu masu garkuwa da mutane a Jibia.
Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun ceto mutane 14 yayin da daya ya rigamu gidan gaskiya saboda harbin yan bindigar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng