An kashe wani Ango a daren farko Yayin da yake ƙoƙarin hana ayi ma Amaryarsa fyaɗe
- Wani sabon ango ya gamu da ajalinsa a darensa na farko bayan wasu da ake zargin 'yan fashi ne suka yima gidanshi tsinke.
- 'Yan fashin sun kashe matashin angon ne yayin da yake ƙoƙarin hanasu yima sabuwar amaryarsa fyaɗe.
- Lamarin ya faru ne a garin Gwashi dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
An kashe wani ango a darensa na farko bayan aurensa yayin da yake ƙoƙarin hana wasu 'yan fashi yima sabuwar amaryar sa fyaɗe.
KARANTA ANAN: Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun kashe matashin angon har lahira a Jihar zamfara.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Gwashi dake karamar hukumar Bukkuyum, a jihar Zamfara.
Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta twitter mai suna, Yusuf Anka, ya turo hotunan jana'izar angon.
KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Gwamnati ta dakatad da jiragen Azman daga tashi
Yusuf Anka ya ce:
"Gawar sabon matashin ango kenan lokacin da ake saka shi a cikin makwancinsa. Wasu 'yan fashi ne suka kashe shi har lahira ya yin da yake ƙoƙarin kare martabar sabuwar Amaryar sa da mutanen ke kokarin yiwa fyaɗe a cikin gidan aurensu."
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta addaba a arewacin Najeriya.
A wani labarin kuma Ministan Buhari ya bayyana yadda tsohon Shugaban hukumar EFCC, Magu zai kare
Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya tabo batun tsohon shugaban hukumar EFCC da aka tsige, Ibrahim Magu.
A 2020 Abubakar Malami ya kai karar Ibrahim Magu wajen mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari , wannan ya sa aka kore shi daga ofis.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.
Asali: Legit.ng