Abia: Dakarun Sojoji Sun Far wa Ƴan Bindiga, An Fara Musayar Wuta Mai Zafi
- Dakarun rundunar soji sun kai samame wani sansanin ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Isiala Ngwa a jihar Abia
- An ruwaito cewa sojojin sun fara artabu da ƴan ta'addan a Mbata da ke kauyen Umuchima ranar Litinin, 25 ga watan Disamba
- Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Gwamna Alex Otti ya yi alƙawarin tabbatar da tsaro a jihar Abia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Rahotanni daga jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna cewa sojoji sun yi arangama da ƴan bindiga da safiyar yau Litinin.
Lamarin ya faru ne da dakarun rundunar Birged ta 14 da ke zaune a Ohafia suka kai samame kan ƴan bindigar a Mbata, kauyen Umuchima a ƙaramar hukumar Isiala Ngwa.
Sojoji sun kai samame maɓoyar ƴan binidga
The Nation ta ce wasu rahotanni da ke yawo sun nuna cewa tun karfe 6:00 na safiya motocin Hilux 15 na sojoji da motocin sulƙe suka isa garin Umuchima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce dakarun sojojin sun shiga yankin ne da nufin murkushe wasu ƴan bindiga da suka yi sansani a kusa da kogin da ya yi iyaka tsakanin Abia da jihar Imo.
Bugu da ƙari, rahotanni sun nuna cewa dakarun sojoji sun karɓe iko da dukkan hanyoyin zuwa da na dawowa daga kauyen.
Yadda sojoji suka ke musayar wuta da miyagu
Jami'an sojojin sun raba kansu, wasu sun tsaya sun tare hanyar shiga da fita, wasu kuma sun shiga sun fara artabu da ƴan bindigar.
Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton, mutane na jin ƙarar harbe-harben bindiga wanda ke nufin sojojin na ci gaba da gwabzawa da ƴan ta'addan.
Sai dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar sojojin kasa ko gwamnatin jihar Abia kan lamarin har kawo yanzu.
Wannnan dai na zuwa ne bayan alkawarin da Gwamna Alex Otti ya dauka na inganta tsaro yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin hukumomin tsaro.
Yan bindiga sun farmaki ƴan sanda
A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an ƴan sanda a jihar Abia.
Ƴan bindigan sun farmaki ƴan sandan ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamban 2024 a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar.
Asali: Legit.ng