Sojojin Sama Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Boko Haram a Wani Hari
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare kan ƴan ta'addan Boko Haram da ke yankin tafkin Chadi
- Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da lalata ma'ajiyar abincinsu a hare-haren da aka kai musu ta sama
- Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin saman ya bayyana cewa an kai hare-haren ne bayan gudanar da bincike mai zurfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai farmaki kan ƴan ta'addan Boko Haram.
Dakarun sojojin sun lalata ma'ajiyar abincin ƴan ta'addan, tare da kashe wasu da dama a wani harin da suka kai ta sama a Jubillaram da ke yankin Tumbuns na tafkin Chadi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), Olusola Akinboyewa, ya fitar ranar Litinin a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kai hari kan ƴan Boko Haram
Olusola Akinboyewa ya ce jirgin sojojin saman ya kai harin ne a ranar 23 ga watan Nuwamba, a wurin da aka gano ta hanyar bincike mai zurfi, rahoton Leadership ya tabbatar.
Ya ce wurin ya kasance muhimmin wajen ajiyar abinci da kuma mafaka ga kwamandojin ƴan ta’adda da mayaƙa.
Ya ƙara da cewa bayanan sirri sun alaƙanta ƴan ta’addan da ke wurin da hare-hare baya-bayan nan, ciki har da harin da aka kai wa sojoji a Kareto a ranar 16 ga watan Nuwamba.
"Lalata maɓoyar ƴan ta'addan, ciki har da ma'ajiyar abincinsu ya kawo musu cikas wajen gudanar da harkokinsu."
"Yayin da hallaka ƴan ta'adda masu yawa ya rage musu ƙarfin kai hare-hare a nan gaba."
- Olusola Akinboyewa
Sojojin sama sun farmaki ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng