Mai Dakin Tinubu Ta Jagoranci Yaki da Cin Zarafin Mata
- Matar shugaban kasa, Remi Bola Tinubu ta mika bukatar a gaggauta kawo karshen tauye hakkin mata da ake yi a duniya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake bikin ranar yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata na kwanaki 16 domin wayar da kai kan illar cin zarafin
- Sanata Remi Tinubu ta bayyana takaicin yadda mata a Najeriya, ke fuskantar cin zarafin musamman a kauyuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai dakin shugaban kasa, Oluremi Bola Tinubu ta jaddada muhimmancin yaki da cin zarafin mata.
Ta fadi matsayarta ne a lokacin da aka fara bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya na kwanaki 16.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanata Remi Tinubu ta ce akwai bukatar gaggauta hukunta masu zarafin mata domin dakile lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Remi Tinubu ta fusata da cin zarafin mata
Channels Televsion ta wallafa cewa Sanata Remi Tinubu ta ce cin zarafin mata babbar illa ce da ke barazana da ga duniya.
Ta ce ana yawan cin mutuncin mata a duniya, inda aka ruwaito cewa kowace mace daya a cikin uku ta fuskanci cin zarafin.
‘Ana cin zarafin mata a Najeriya,’ Remi Tinubu
Mai dakin shugaban kasa ta lissafo wasu daga cikin hanyoyin da ake bi wajen cin zarafin mata a kasar nan.
Ta ce wasu daga cikin kalubalen da mata ke fuskanta sun hada da aurar da yara kanana, yi wa mata shayi da sauransu.
Remi Tinubu ta ce;
“Duk da ana samun cigaba, da yawa daga cikin mata da yara, musamman a kauyuka su na fadawa tarkon cin zarafin da rashin samun adalci."
Remi Tinubu ta gargadi malamai
A baya mun ruwaito cewa uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta gargadi malamai da ke aibata shugabanni da sauran masu mulki a kasar nan da cewa su daina wannan dabi'a.
Sanata Remi Tinubu ta yi takaicin yadda malamai su ka koma tsinewa shugabanni a maimakon su rika yawaita yi masu addu'o'in samun nasara da yi masu nasiha kan dabarun mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng