Ministan Buhari Ya Fadi Shugabannin da Suka Fi Gwamnoni Kwarewa a Karbar Rashawa

Ministan Buhari Ya Fadi Shugabannin da Suka Fi Gwamnoni Kwarewa a Karbar Rashawa

  • Tsohon ministan kwadago, Chris Ngige, ya yi tir da wasu ciyamomi wadanda ya ce sun fi gwamnoni cin hanci da rashawa
  • Chris Ngigge ya ce wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomin sun fi gane mallakar gidaje a Abuja, Legas da kasar waje
  • Tsohon ministan ya ce rashin bin doka da tsarin mulki daga gwamnonin ne ya kawo matsaloli a tsarin kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Sanata Chris Ngige, tsohon ministan kwadago da ayyuka, ya ce akwai shugabannin da suka fi gwamnoni karbar cin hanci da rashawa.

Tsohon ministan a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ya ce wasu shugabannin kananan hukumomi sun fi gwamnonin jihohi cin hanci.

Tsohon ministan BNuhari, Chris Ngige ya yi magana kan cin hanci da rashawa a tsakanin ciyamomi
Chris Ngige, tsohon ministan Buhari ya ce cin hanci ya yi katutu a tsakanin ciyamomi. Hoto: @LabourMinNG
Asali: Twitter

Tsohon minista ya caccaki wasu ciyamomi

Chris Ngige ya ce waɗannan shugabannin kananan hukumomin suna amfani da kudaden jama'a wajen sayen gidaje a Legas, Abuja da ma kasashen waje, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya yi magana, kwanaki 10 da sauka an fara bincikensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce kwata kwata ire iren wadannan ciyamomin ba sa damuwa da inganta asibitoci, makarantu ko wasu ababen more rayuwa a yankunansu.

Ngige ya yi ƙorafi kan yadda aka wofantar da fiye da cibiyoyin kiwon lafiya 15,000 da aka gina a matsayin ayyukan mazabu a fadin Najeriya.

Chris Ngige ya nemi kotu ta janye hukuncinta

Haka nan ya yi kira ga Kotun Koli da ta sake duba hukuncinta kan ’yancin gashin kai na kananan hukumomi, wanda yake ganin bai kamata a yanke irin hukuncin ba.

Tsohon minista ya yi ikirarin cewa hukuncin ya saba da Kundin Tsarin Mulki na 1999, musamman Sashe na bakwai game da gudanarwar kananan hukumomi.

Ngige ya ce hukuncin yana ƙoƙarin rage muhimmancin da kananan hukumomi ke da shi wanda kuma ya kamata su kasance a ƙarƙashin ikon jihohi.

Tsohon ministan kwadago ya dura kan gwamnoni

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya yi murabus mai gidansa na tsaka da alhinin mutuwar matarsa

Ya kuma alakanta tabarbarewar tsarin gudanar da kananan hukumomi ga ayyukan wasu bata garin gwamnoni da ke karkatar da kudaden kananan hukumomi don amfanin kansu.

Ngige ya ce har sai gwamnoni sun kiyaye doka da oda kuma majalisun jihohi sun fara aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata ne tsarin kananan hukumomi zai daidaita.

Kalubalen da kananan hukumomi ke fuskanta

A wani labarin, mun ruwaito cewa kananan hukumomi 774 na Najeriya sun fuskanci kalubale bayan hukuncin kotun koli da ya ba su 'yancin cin gashin kai.

Daga cikin matsalolin da kananan hukumomin suka fuskanta akwai rashin sanin makaman aiki, cin hanci da rashawa da sauransu kamar yadda wata hukuma a Kano ta sanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.