'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Banga a Wani Harin Kwanton Bauna
- Ƴan bindiga sun kai harin kwanton ɓauna kan jami'an tsaro na ƴan banga a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja
- Tsagerun sun hallaka ƴan banga mutum bakwai bayan an kwashi lokaci ana musayar wuta a tsakanin ɓangarorin guda biyu
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar harin da aka kai kan ƴan banga masu raka manoma ɗauko amfanin gona
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wasu ƴan bindiga sun kashe ƴan banga bakwai a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Ƴan bindigan sun kashe ƴan bangan ne waɗanda ke raka manoma kai amfanin gona a Makogi/Ungwan Elbi da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Ƴan bindiga sun kai wa ƴan banga hari
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƴan bangan sun raka buhunan masara sama da 50 da aka girbe a garin Wamba zuwa Bangi hedkwatar ƙaramar hukumar, inda ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bangan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan, suka jikkata da dama daga cikinsu.
Duk da haka, ƴan bindigan sun kashe mutum bakwai daga cikin ƴan banga.
Wani magidanci mai suna Salihu Wamba ya bayyana cewa babu wani abu da ya samu manoman, domin sun isa ƙauyen ne kafin ƴan bindigan su yi wa ƴan bangan kwanton ɓauna a hanyarsu ta dawowa.
Ƴan sanda sun yi magana kan harin
Jaridar Premium Times ta ce jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce waɗanda aka kashe ba manoma ba ne, ƴan banga ne.
"Ƴan bindiga sun yi wa ƴan banga daga Wamba kwanton ɓauna a tsakanin Makogi/Ungwan Elbi. Abin takaici sun hallaka mutum bakwai daga cikinsu."
- Wasiu Abiodun
Miyagun yan bindiga sun hallaka lauya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun harbe wani matashin lauya, Barista Mike Ofikwu a garin Otukpo na jihar Benue.
Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindiga sun harbe lauyan wanda ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ne da daddare a kusa da gidansa da ke kan titin Otukpa a Otukpo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng