Kotu Ta Shirya Zama Kan Karar da aka Shigar Kan Arewa24 Bisa Zargin Saba Ka'idojin Najeriya
- An maka tashar Arewa24 a gaban kotu kan gudanar da aikinta ba tare da bin ka'idojin doka ba a Najeriya
- Kwamitin amintattu na ƙungiyar masu shirya watsa labarai ta Arewa, NBMOA shi ya shigar da korafin a gaban Babbar Kotun
- Wannan na zuwa ne bayan korafin da aka shigar kan zargin tashar Arewa24 da gudanar da aiki ba tare da lasisi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta shirya yin zama kan korafin da aka shigar da tashar Arewa24.
Kotun za ta fara sauraran karar da Kwamitin amintattu na ƙungiyar masu shirya watsa labarai ta Arewa, NBMOA ta shigar.
An maka tashar Arewa24 a gaban kotu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu a yau Lahadi 24 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shigar da korafin ne kan tashar talabijin ta Arewa24 da wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati bakwai da zargin aiki ba bisa ƙa’ida ba.
Daga cikin wadanda ake karar sun haɗa da Hukumar Yaɗa Labarai ta Kasa (NBC) da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya.
Sai kuma Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Najeriya (ARCON) da Hukumar ba da Kariya ga ta Jama’a da MultiChoice Nigeria da StarTimes Nigeria da sauransu.
Shugaban kungiyar ya magantu kan shari'ar
Shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar NBMOA, Dr Ahmed Tijjani Ramalan ya ce suna kalubalantar ba da lasisi ne da kuma ayyukansu ba ba tare da bin ka'ida ba.
“Wannan batu da ke ƙalubalantar ba da lasisi, da kuma yadda ake gudanar da ayyukan waɗanda ake ƙara, ya jaddada ƙudirin hukumar ta NBMOA wajen bin doka da oda da ka'idojin watsa shirye-shirye na NBC da kuma yarjejeniyar manufofin abubuwan cikin gida da na Gwamnatin Tarayya."
- Ahmad Tijjani Ramalan
Kungiya ta shigar da Arewa24 kara a kotu
A baya, kun ji cewa Kungiyar masu kafafen yada labarai ta NBMOA ta sake maka tashar nan ta Arewa24 a gaban kotu bisa zargin aiki babu lasisi.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Alhaji (Dr.) Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana cewa Arewa24 ta zama barazana ga Arewa.
Asali: Legit.ng