Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur, Ta Saukakawa Yan Kasuwa daga N990
- Matatar man Aliko Dangote ta dauki matakin rage farashin man fetur ga yan kasuwa domin saukaka musu da yan kasa baki daya
- Matatar ta ɗauki matakin ne domin saukakawa yan kasa da ba yan kasuwa damar samun rarar N20 a kan kowace lita
- Wannan na zuwa ne yayin da yan kasa ke kokawa kan halin kunci da ake saboda karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ana kuka da tsadar mai a Najeriya, matatar Aliko Dangote ta rage farashin mai ga yan kasuwa.
Matatar ta rage farashin fetur ga yan kasuwar daga N990 da ta sanar a farkon watan Nuwambar 2024 da muke ciki zuwa N970.
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai kula da bangaren sadarwa, Anthony Chiejina ya fitar da TheCable ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da aka fitar a yau Lahadi 24 ga watan Nuwambar 2024 ta ce ragin zai taimakawa yan kasuwa.
Chiejina ya ce aƙalla yan kasuwar za su samu rarar N20 kan kowace lita da ake daukowa daga ma'adanar Lekki.
Musabbabin Matatar Dangote na rage farashin mai
Ya ce an dauki matakin ne domin saukakawa yan kasa saboda goyon baya da suke ba matatar Dangote domin ganin ta samu cigaba, cewar Vanguard.
"Dadi da kari, an yi hakan ne domin nuna godiya da gwamnati kan goyon baya da kuma matakan da take dauka wurin inganta kayan cikin gida."
"Matatarmu ba za ta gajiya ba wurin samar muku da ingantaccen kaya da za su zama daidai da wadatuwar al'umma."
- Anthony Chiejina
Dangote zai sayi danyen mai daga Amurka
Kun ji cewa Matatar Dangote ta na jiran danyen mai daga kasar waje duk da kokarin gwamnatin Najeriya ya sayar mata kaya da sauki.
A baya ne gwamnatin kasar nan da Dangote su ka cimma matsaya kan sayarwa matatar danyen fetur da Naira a maimakon Dala.
Sai dai an samu rahoton za a shigowa da Dangote da danyen mai akalla ganga miliyan biyu a wata mai kamawa.
Asali: Legit.ng