Gwamna Ya Roki 'Yan Kwadago Su Hakura da Shiga Yajin Aiki
- Ƙungiyoyin ƙwadago na shirin fara yajin aiki gargaɗi na kwana biyu a jihar Cross Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
- Gwamnan jihar, Bassey Edet Odu, ya buƙaci ƴan ƙwadagon da su haƙura da shiga yajin aikin da suke shirin farawa
- Ya bayyana cewa zsi ci gaba ɗa maida hankali wajen inganta jin daɗi da walwalar ma'aikatan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Cross Rivers - Gwamnan Cross Rivers, Bassey Edet Otu, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago na jihar da su haƙura da shiga yajin aiki.
Gwamna Bassey Otu ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon da su sake duba yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da za su fara daga ranar Lahadi, 24 ga Nuwamba zuwa Talata 26 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Peter Odey, ya yi wannan roko ne a yayin wani taro da aka gudanar a filin wasa na U.J. Esuene dake Calabar ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otu ya yi kira ga ƴan ƙwadago
Ya buƙaci shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da su janye yajin aikin da suke shirin yi a fadin jihar tare da haɗa kai da gwamnan a ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma.
Peter Odey ya ƙara jaddada aniyar Gwamna Otu ta samar da ingantacciyar jihar Cross River ga ɗaukacin mutanenta, rahoton The Nation ya tabbatar.
Peter Odey ya bayyana cewa gwamnan ya jajirce wajen inganta halin da ma'aikata da waɗanda suka yi ritaya suke ciki, ta hanyar biyan basussukan giratuti, biyan kuɗin fansho a kan lokaci da yin ƙarin girma.
"Gwamna Otu ya ba da muhimmanci sosai ga jin daɗin ma’aikata."
- Peter Odey
Ya kuma tabbatar da cewa jihar Cross Rivers na da aniyar samar da mafi ƙarancin albashin da ya zarce N70,000.
Gwamnan Cross Rivers ya yi ƙarin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Cross Rivers Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma'aikata jiharsa.
Gwamna Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar Cross Rivers inda ya ce ya yi hakan ne duba da halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng