Ana Rigimar Lamido da Wamakko, Sarkin Musulmi Ya Fadi 'Yan Siyasan da Za a Yi Koyi da Su
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ba Sokoto shawarar abin da za ta koya daga makwabciyarta jihar Kebbi
- Sarkin Musulmin ya bayyana cewa ya kamata jihar Sokoto ta koyi halin siyasa na haɗin kai da Kebbi take da shi
- Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana hakan a matsayin wani abu na musamman wanda ya kamata a yi koyi da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana abin da ya kamata Sokoto ta koya daga makwabciyarta jihar Kebbi.
Sarkin Musulmin ya buƙaci Sokoto da ta koyo irin salon siyasar haɗin kai da jihar Kebbi take da shi.
Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana hakan ne a wajen lakcar da aka shirya ta Malam Abdullahi Fodio ta shekarar 2024 a birnin Kebbi na jihar Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya yabi ƴan siyasan Kebbi
Sarkin Musulmin ya yi matuƙar farin ciki da halartar tsofaffin gwamnonin Kebbi uku da suka zauna kafaɗa da kafaɗa da gwamna mai ci a wajen taron.
Alhaji Abubakar Sa'ad III ya bayyana lamarin a matsayin abu na musamman wanda ya cancanci a yaba masa.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa dukkanin gwamnonin sun ajiye saɓanin siyasa a gefe, sun haɗu a waje ɗaya ta hanyar halartar taron domin cimma manufa guda ta tunawa da Abdullahi Fodio.
"Wannan abu ne da ya kamata mu koyo daga Kebbi. A yau mun ga dukkanin tsofaffin gwamnonin sun zauna tare da gwamna mai ci a wajen wannan taron mai tarihi."
"Taron ya haɗa sarakunan gargajiya daga sassan daban-daban na ƙasar nan."
- Alhaji Sa'ad Abubakar III
Wannan, a cewarsa yana nuna soyayya, juriya, fahimtar juna a tsakanin ƴan Najeriya ba tare da la’akari da al’ada, ƙabila ko addini ba.
Sarkin Musulmi ya faɗi ƙalubalen shugabanni
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa batun almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta, babban ƙalubale ne ga shugabanni a Arewacin Najeriya.
Sarkin Musulmi ya nuna cewa akwai miliyoyin irin waɗannan yara da suke yawo a garuruwa, birane da ƙauyuka a faɗin yankin.
Asali: Legit.ng