Gwamnati Ta Kori Ma'aikata Masu Digirin Togo da Benin? An Karyata Tsohon Sanata
- Gwamnatin tarayya ta musanta rahoton korar dimbin ma’aikatan gwamnati da suka samu digiri a jamhuriyar Benin da Togo
- A cewar wata sanarwa da hukumar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta fitar, babu wata takarda da ta ce a dauki wannan mataki
- Shehu Sani ne ya yi wannan zargin, inda ya nemi gwamnati da ta janye matakin korar ma’aikatan da ke da digiri dan kwatano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya sun shiga damuwa kan yiwuwar rasa ayyukansu bayan rahoton korar masu takardar digiri daga jami’o’in Benin da Togo.
Wannan fargabar ta karu bayan tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya wallafa sako a kafar sada zumunta ta zamani inda ya yi Allah wadai da korar ma’aikatan.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Shehu Sani ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Masu digiri daga Benin da suka yi aure suna da yara, sun fi jin radadin wannan korar. Ina kira ga gwamnati da ta samar da wata hanya ta ilimi don gyara matsalar."
Gwamnati ta karyata ikirarin Sehu Sani
Sai dai, hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya ta karyata zargin cewa an kori ma’aikata masu digiri 'dan kwatano'.
Shugaban sashen watsa labarai, Taiwo Hassan, ya ce babu wani rahoto ko shawara da aka aika musu kan wannan batu a yanzu a cewar rahoton Vanguard.
Hassan ya kara da cewa, “Idan an kawo mana rahoto, za mu duba shi bisa ka’idoji da tsari kafin daukar mataki.”
Babu shirin korar ma'aikatan gwamnati
Ya bayyana cewa korar ma’aikata tana da tsari, ciki har da gayyatar wadanda abin ya shafa don bayar da hujjojin takardunsu kafin yanke shawara.
Hukumar ta jaddada cikakken iko da ta ke da shi kan daukar aiki da sallama, tare da tabbatar da babu wani mataki na korar ma’aikata a boye.
Mahukuntan sun tabbatar wa jama’a cewa za a sanar da su idan an samu wani sauyi, tare da karyata rade-radin korar ma’aikata a halin yanzu.
NYSC: Shehu Sani ya ba gwamnati shawara
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani kan ƙarin alawus da gwamnatin tarayya ta yi wa matasa ƴan NYSC daga N33,000 zuwa N77,000.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce ƙarin alawin abin a yaba ne amma mata ƴan NYSC sun cancanci fiye da hakan la'akari da dawainiyar da ke kansu.
Asali: Legit.ng