Kaduna: Shugaban Kungiyar Nasril Islam Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekaru 93
- Fitaccen malami kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna
- Marigayin mai suna Jafaru Makarfi ya rasu ne a daren jiya Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 93
- Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayin a yau Lahadi 23 ga watan Nuwambar 2024 a masallacin Sultan Bello
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - An shiga jimami bayan sanar da rashin babban malamin kuma shugaban kungiyar JIN, Jafaru Makarfi a jihar Kaduna.
Marigayin ya rasu ne a daren jiya Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024 a Kaduna yana da shekaru 93 a duniya.

Source: Original
Malamin Musulunci ya rasu a Kaduna
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daya daga cikin iyalansa, Suleman Abdulkadir ya fitar, cewar Premium Times.
Abdulkadir wanda shi ne Garkuwan Zazzau ya ce marigayin kafin rasuwarsa ya rike shugabancin kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Kaduna.
Garkuwan Zazzau ya sanar da cewa marigayin ya rasu ne a daren jiya Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin kafin rasuwarsa ya rike mukamin kwamishina a tsohuwar jihar Kaduna, cewar Daily Post.
An sanar da lokacin sallar jana'izar marigayin
"Tsohon ma'aikaci ne a ma'aikatar sufurin jiragen kasa (NRC) inda ya fara aiki a shekarar 1950 kuma ya shafe shekaru 40."
"Marigayin ya rasu ya bar iyalansa da 'ya'ya shida, muna tura sakon ta'aziyya ga iyalansa da JNI da al'ummar Musulmi da abokan arziki."
- Suleman Abdulkadir
Abdulkadir ya tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izarsa a yau Lahadi da misalin karfe 1.00 na rana a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
Tsohon sanata a Kano ya kwanta dama
Kun ji cewa fitaccen dan siyasa a jihar Kano, Sanata Aminu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Marigayin ya rike muƙamin sanata a jamhuriya ta uku karkashin jam'iyyar SDP bayan rasa tikitin takarar gwamna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 79.
Asali: Legit.ng

