Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Kwanaki bayan Kammala Taron G20 a Brazil

Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Kwanaki bayan Kammala Taron G20 a Brazil

  • Jirgin shugaban ƙasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja
  • Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya ne bayan ya halarci taron ƙasashen G20 da aka gudanar a ƙasar Brazil
  • A yayin da Tinubu yake a Brazil ya gudanar da tarurruka masu muhimmanci tare da rattaɓa hannu kan yarjeniyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya iso gida Najeriya daga ƙasar Brazil.

Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya daga Brazil ne bayan ya halarci taron shugabannin ƙasashen G20.

Tinuɓu ya dawo Najrriya
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya daga Brazil Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya

Shugaba Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da yammacin ranar Asabar, cewa rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya samu tarba daga tawagar jami’an gwamnati da sauran manyan baƙi, sa’o’i bayan ya bar filin jirgin saman Galeao Air Force Basa (SBGL), da ke Rio de Janeiro, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ke yi don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

Tinubu ya halarci taron inda a wajen ya amince da ƙawancen duniya domin yaƙi da yunwa da fatara.

Shugaban na Najeriya ya kuma tattauna da shugabar asusun lamuni na duniya (IMF), Kristalina Georgieva, wacce ta yaba da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya yi a fannin tattalin arziƙi.

Wata babbar tawaga da ta haɗa da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ministan kiwon dabbobi, Mukhtar Idi Maiha, ministan fasaha, yawon shaƙatawa da al'adu, Hannatu Musa Musa na daga cikin waɗanda suka raka Tinubu wajen taron.

Minista ya faɗi dalilin shan wuya a mulkin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan kudi da harkokin tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana dalilin da ya sa manufofin shugaban kasa, Bola Tinubu suka kawo wahala a Najeriya.

Edun ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin Tinubu sun haifar da walaha, kunci da tsadar rayuwa ne saboda gwamnatocin da suka gabata ba su ɗauki matakin da ya dace ba.

Ministan ya bayyana cewa duka da wahalar da ake sha a yanzu, lokacin jin daɗi na nan zuwa nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng