“Ba Mu da Shalele’: Kungiyar ACF Ta Fadi Yadda Ta Yiwa Buhari bayan Sukar Tinubu
- Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta mayar da martani kan masu cewa tana sukar gwamnatin Bola Tinubu saboda dan Kudu ne
- Kungiyar ta musanta wannan labari inda ta ce yadda take sukar Tinubu haka ta yiwa gwamnatin Muhammadu Buhari a mulkinsa
- Wannan na zuwa ne bayan sukar tsare-tsaren Tinubu inda ta ce suna jawo wahalhalu musamman ga yan yankin Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi magana kan sukar Bola Tinubu da take yi.
Kungiyar ACF ta ce tana caccakar gwamnatin Tinubu kamar yadda ta yiwa Muhammadu Buhari lokacin mulkinsa.
Kungiyar ACF ta magantu kan zargin sukar Tinubu
Sakataren kungiyar, Murtala Aliyu shi ya bayyana haka a yayin hira da gidan talabijin na Arise.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliyu ya ce kungiyar za ta iya zama ta siyasa amma kuma ba ta da wani bangare ko dan siyasa da take goyon baya.
Ya ce rashin adalci ne a ce wai kungiyar tana caccakar shugaban kasa kawai domin ya fito daga yankin Kudancin kasar, cewar TheCable.
ACF ta fadi yadda ta soki gwamnatin Buhari
"Ina tunanin rashin adalci ne wai muna caccakar gwamnati saboda dan Kudu ne yake mulkin kasar."
"Muna daga cikin manyan wadanda suke sukar gwamnatin da ta shude da dan Arewa ke mulki, akwai hujjoji suna nan."
"Muna yawan jan hankulan gwamnati kan wasu abubuwa da suka yi da neman kawo gyara idan akwai bukatar hakan."
Murtala Aliyu
Kungiyar ta ce ba ta daukar bangare a siyasa kuma har yanzu ba ta gaba da kowa ciki har da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Zaben 2027: Kungiyar ACF ta dakatar da shugabanta
Kun ji cewa bayan sake bayanai kan zaben 2027 mai zuwa, Kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF ta dakatar da shugabanta.
An dakatar da Mamman Mike Osuman ne bayan ya yi wasu kalamai game da zaben 2027 inda ya ɗan yankin Arewa za su zaba.
Osuman ya koka kan yadda tsare-tsaren Bola Tinubu suka rikita kasar musamman yankin Arewa da al'ummarta.
Asali: Legit.ng