Gwamna Soludo Ya Cika Umarnin Tinubu, Ma'aikata Sun Fara Walwala a Jihar Anambra
- Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya tabbatar da fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000 tun a watan Oktoba
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Dr. Law Mefor ya ce rahoton da ake yaɗawa cewa Anambra ba ta cikin jihohin da suka yi ƙarin albashi ba gaskiya ba ne
- Ya ce tuni ma'aikata suka fara cin moriyar sabon albashin kuma su kansu ƴan fansho an masu ƙari domin inganta walwalarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da cewa tuni ta fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Dr. Law Mefor ya fitar ranar Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024.
Ya ce Gwamna Charles Soludo ya cika umarnin Gwamnatin Bola Tinubu na fara biyan sabon albashi da nufin inganta rayuwar ma’aikata, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Soludo ya musanta ikirarin wani rahoto
Kwamishinan ya kuma karyata rahoton da ke yawo a soshiyal midiya, wanda ya cire jihar Anambra daga jerin jihohin da suka fara biyan sabon albashin.
Dr. Mefor ya ce rahoton ba gaskiya ba ne domin Gwamnatin Soludo ta fara biyan albashin N70,000 tun a karshen watan Oktoban 2024.
Ya nanata cewa gwamnatin ta aiwatar da sabon albashin domin cika alkawarin da ta ɗauka tun lokacin kamfe na inganta rayuwa da walwalar ma'aikatanta.
Gwamnan Anambra na tare da ma'aikata
A cewarsa, gwamnatin Anambara za ta yi duk mai yiwuwa wajen tallafawa ma'aikata, inda ya ƙara da cewa ƙarin albashin zai taka rawa a halin da ake ciki.
Kwammishinan ya ce:
"Gwamna Soludo ya ɗauki ma'aikata a matsayin abokan aiki kuma ba wai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi kaɗai ba, yana ƙoƙarin biyan kowa haƙƙinsa kafin ko ranar 25 na kowane wata."
"Bayan nan ya karawa ƴan fansho kudin da ake ba su duk ƙarshen wata domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu a jihar Anambra."
Gwamna Adeleke zai fara biyan N75,000
A wani rahoton, an ji cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya sanar da sabon mafi karancin albashin da zai fara biyan ma'aikatan gwamnati.
A wata sanarwa, kwamishinan yaɗa labaran Osun ya ce Gwaman Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon albashi mafi kanƙanta.
Asali: Legit.ng