Majalisar Dattawa Ta Nuna Damuwa kan Boko Haram, Ta ba Sojoji Umarni

Majalisar Dattawa Ta Nuna Damuwa kan Boko Haram, Ta ba Sojoji Umarni

  • Majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a wasu ƙananan hukumomin jihar Borno
  • Sanata Tahir Monguno ya gabatar da ƙudirin neman a tura isassun jami'an tsaro zuwa ƙananan hukumomin da ƴan Boko Haram ke cin karensu babu babbaka
  • Majalisar dattawan ta yi kira ga rundunar sojojin da ta tura isassun jami'an tsaro domin murƙushe masu tayar da ƙayar baya a ƙananan hukumomin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi magana kan batun wasu ƙananan hukumomi da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram a jihar borno.

Majalisar dattawan ta yi kira ga sojojin Najeriya da su tura isassun jami’ai domin ƙwato ƙananan hukumomin Abadam da Marte, waɗanda ake cewa mayaƙan Boko Haram ne ke iko da su.

Majalisar dattawa ta damu kan Boko Haram
Majalisar dattawa ta bukaci a tura karin jami'an sojoji zuwa Borno Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta koka kan Boko Haram

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kwamandan 'yan ta'adda da wasu 114

Majalisar dattawan ta yi wannan kiran ne a yayin zaman da ta yi na ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Dattawa ta yaba da sadaukarwar da sojoji suka yi wajen yaƙar ta’addanci, amma ta nuna damuwa kan yadda Boko Haram ke ci gaba da iko a ƙananan hukumomin biyu.

Majalisar ta cimma matsayar ne biyo bayan kudirin da Sanata Mohammed Tahir Monguno, ya gabatar na buƙatar tura isassun jami'ai zuwa ƙananan hukumomin.

Sanata Monguno ya nuna damuwarsa game da rashin sojoji a ƙananan hukumomin Guzamala, Abadam, da Marte, wadanda galibin al’ummarsu manoma ne.

Wace matsaya majalisar ta cimmawa?

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya godewa Sanata Monguno kan wannan ƙudiri da ya gabatar, ya kuma yabawa sojoji bisa sadaukarwar da suke yi.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su maido da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan 'yan ta'addan Boko Haram sun farmaki jami'an NSCDC

A matsayar da ta cimmawa, majalisar ta umarci kwamitocinta na sojoji da sojojin Sama da su tabbatar da aiwatar da kiran da ta yi na ƙara tsaro a ƙananan hukumomin Abadam da Marte.

Tinubu ya buƙaci a amince da shugaban sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin hafsan sojojin kasa (COAS).

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma'a, 22 ga wstan Nuwamba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng