Bayan Pantami, Sarkin Musulmi Ya Ba Gwamnan Jihar Kebbi Babbar Sarauta a Najeriya

Bayan Pantami, Sarkin Musulmi Ya Ba Gwamnan Jihar Kebbi Babbar Sarauta a Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ba gwamnan jihar Kebbi sarautar Gwarzon Daular Usmaniyya
  • Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya miƙawa gwamnan takardar naɗa shi sarautar a madadin sarkin Musulmi
  • Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnati da mutanen Kebbi za su samu lokaci su je fadar sarkin Musulmi domin yin godiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya naɗa gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris a sarautar gwarzon daular Usmaniyya.

Sarkin Musulmin ya karrama gwamnan da wannan sarauta ne saboda ɗumbin gudummuwar da yake bayarwa wajen taimakon al'umma a kasar nan.

Gwamna Nasir Idrisda Sultan.
Sarkin Musulmi ya naɗa gwamnan Kebbi a sarautar Gwarzon Daular Usmaniyya Hoto: Daular Usmaniyya, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

Wakilin Sultan kuma sarkin Argungun, Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya gabatar da takardar naɗin sarautar a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, Leadership ta kawo.

Kara karanta wannan

Ana zargin alaka ta yi tsami tsakanin Namadi da Badaru, Gwamna ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya ba gwamna sarauta

Ya ce sarautar gwarzon daular Usmaniyya ana ba da ita ne ga wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon mutane a jiharsa da kuma kasarsa.

Sarkin Argungu ya ce masarautar Sarkin Musulmi tana sane da kyautatawa, taimakon da gudummuwar da gwamnan yake bayarwa wajen inganta rayuwar al'umna.

"Majalisar masarautar sarkin Musulmi za ta sanar da ranar da za a naɗawa gwamnan rawanin sarautar ga gwamnatin Kebbi nan ba da jimawa ba," in ji shi.

Gwamnan Kebbi ya ji daɗin sarautar

.Da yake karbar takardar, Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya godewa masarautar Sarkin Musulmi bisa ganin ya cancanta ta ba shi wannan sarauta mai ƙima.

Ya ce gwamnati Kebbi da al’ummar jihar Kebbi za su sanya lokaci su je godiya fadar Sarkin Musulmi a Sakkwato domin nuna jin daɗinsu da naɗin.

Pantami ya zama Majidaɗin Daular Usmaniyya

A wani rahoton, an ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje Farfesa Isa Ali Pantami da sarauta a daular Usmaniyya

Sultan Muhammad Sa'ad ya ba Farfesa Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniyya a ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262