'Yan Takarar Gwamnan Ondo Sun Fadi Matsayarsu kan Nasarar Aiyedatiwa
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya samu goyon baya daga wajen ƴan takarar gwamna 13 da suka fafata a zaɓen Ondo
- Ƴan takarar sun bayyana cewa sun amince da sakamakon zaɓen gwamnan wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024
- Gwamna Aiyedatiwa ya nuna jin daɗinsa kan goyon da suka ba shi inda ya ce ba zai yi wasa da hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Ƴan takarar jam’iyyun siyasar da suka fafata a zaɓen gwamnan jihar Ondo, sun bayyana matsayarsu kan nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Ƴan takarar sun bayyana cewa sun amince da sakamakon zaɓen tare da bayyana shirin su na haɗa kai da Gwamna Lucky Aiyedatiwa domin gina sabuwar jihar Ondo.
Ƴan takarar sun bayyana hakan ne lokacin da suka gana da Aiyedatiwa tare da shugabannin jam’iyyunsu, a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Akure, babban birnin jihar a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan adawa sun amince da nasarar Aiyedatiwa
Sun kuma yi alƙawarin goyon bayan gwamnatin Aiyedatiwa domin ci gaban jihar.
Ƴan takarar na jam'iyyu 13 sun ce sun amince da sakamakon zaɓen gwamnan jihar, sannan suka buƙaci Gwamna Aiyedatiwa da ya dama da sauran jam’iyyun siyasar da suka fafata da shi.
Jam'iyyun da suka halarci taron sun haɗa da Accord (A), AA, APM, NNPP, APP, ADP, ADC, APGA, LP, YP, YPP, BP da ZLP.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi godiya
Da yake mayar da martani, Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa ƴan takarar da shugabannin jam'iyyunsu kan alƙawarin da suka yi na marawa gwamnatinsa baya, inda ya ce ba zai yi wasa da goyon bayansu ba.
Ya bayyana cewa ci gaban jihar abu ne wanda ya zama wajibi kan kowa da kowa don haka ya buƙaci masu ruwa da tsaki su zo a haɗa kai domin cimma hakan.
Rawar da Tinubu ya taka kan nasarar Aiyedatiwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya sake yin magana kan zaben jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Ganduje ya tabbatar da cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara ba tare da saka baki daga fadar shugaban kasa ba.
Asali: Legit.ng