Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutane 14 a Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutane 14 a Jihar Kaduna

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Ungwan Babangida da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna, sun sace mutane 15
  • Wani shugaban matasa, Aminu Khalid ya ce Magajin garin na cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su ranar Alhamis da daddare
  • Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jami'an tsaro su kara zage dantse wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Magajin Garin Ungwan Babangida da wasu mutum 14 a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen tare da sace mutanen a daren ranar Alhamis da ta gabata.

Taswirar jihar Kaduna.
Muyagun ƴan bindiga sun kai farmaki, sun sace Magajin Gari da wasu mutane a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Punch ta ruwaito cewa shugaban matasan Dokan Karji, Aminu Khalid, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka manoma 7, sun ƙona buhunan masara 50 a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace basarake a Kaduna

A cewarsa, maharan sun kutsa cikin kauyen Ungwan Babangida da tsakar dare dauke da manyan makamai, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wannan lamarin ya faru ne sa’o’i 48 bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma hudu a kauyen Libere da ke karamar hukumar Kauru.

“Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a Ungwan Babangida akwai mata uku, da maza tara da suka hada da Magajin Gari mai suna Babangida Sojiji,” in ji Aminu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su leburori ne da suka zo aikin noma daga jihar Jigawa da kuma karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

Ya kamata jami'an tsaro su tashi tsaye

A ruwayar Channels tv, Aminu Khalid ya ce:

"Yankin Kauru na bukatar daukar tsauraran matakan soji kan wadannan 'yan bindigar da suka hana kauyuka da dama zaman lafiya, suna kashe magidanta.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace ƴan uwan ɗan jarida ana tsaka da jimamin rasuwar mahaifiyarsa

"Ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su kara zage dantse wajen daƙile ayyukan wadannan ‘yan ta’adda da suka jefa rayuwar mazauna kauyuka cikin kunci.”

Aminu ya kuma yabawa ‘yan banga bisa yadda suke tunkarar ‘yan fashin dajin, inda ya ce sun dakile yunkurin sace mutane da dama a wasu kauyuka.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, ya ki cewa komai kan lamarin.

Zaman gida ya gagari mazaunan Kaduna

Kun ji cewa mazauna jihar Kaduna sun fara kukan neman dauki bayan yan ta'adda sun matsa da yi masu dauki dai-dai.

Mazauna Dokan Karji a karamar hukumar Kauru da ke jihar sun bayyana cewa yan bindiga sun matsa da kai masu hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262