Obasanjo Ya Gano Matsalar da Ta Hana Najeriya Samun Cigaba
- Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya sake yin magana kan matsalar cin hanci da rashawa da ta addabi Najeriya
- Obasanjo ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin wani mugun abu da dole sai an magance shi kafin a samu ci gaban da ake buƙata a ƙasar nan
- Tsohon shugaban ƙasan ya nuna cewa a lokacin da yake kan mulki ya yi ƙoƙarin ganin an shawo kan matsalar ta cin hanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya bayyana cin hanci da rashawa matsayin wani mugun abu wanda dole sai an kawar da shi kafin a samu wani ci gaba mai ma'ana a ƙasar nan.
Olusegun Obasanjo ya halarci taro a Ibadan
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wajen bikin tunawa da tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, mai shari’a Emmanuel Ayoola, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da bikin ne a cocin Methodist da ke Agodi, Oke Ado a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar Juma’a, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Tsohon shugaban hukumar ta ICPC ya rasu ne a ranar 20 ga watan Agusta, 2024 yana da shekara 90 a duniya.
Me Obasanjo ya ce kan cin hanci da rashawa?
Olusegun Obasanjo ya ce ya yi ƙoƙari a lokacin gwamnatinsa don ganin an dakile cin hanci da rashawa.
"Cin hanci da rashawa mugun abu ne wanda har yanzu muke fama da shi a ƙasar nan."
"Ba wai ICPC da mai shari’a Ayoola ba su yi aikinsu ba, ko kuma ni da na naɗa shi ban yi abin da zan iya yi ba, kawai dai matsin lamba ne daga wannan mugun ciwon na cin hanci da rashawa."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya soki salon mulkin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin da Bola Tinubu ke bi wajen gudanar da gwamnati.
Tsohon shugaban kasan ya yi zargin cewa Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata sahihiyar hanya ta magance matsalolin da su ka damu Najeriya.
Asali: Legit.ng