An Kama Ƙasurgumin Ɓarawon Babur Mai Cakawa Ƴan Acaba Makami a Kai

An Kama Ƙasurgumin Ɓarawon Babur Mai Cakawa Ƴan Acaba Makami a Kai

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Bauchi na nuni da cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wani ƙasurgumin ɓarawon babur
  • Ana zargin ɓarawon mai suna Abdulrashid Abubakar da ƙoƙarin kashe wani dan acaba ta hanyar caka masa makamai a kayi
  • A ranar 21 ga watan Nuwamba yan sanda suka samu kiran gaggawa kan cewa wani ɓarawo ya sace babur a ƙauyen Guru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da satar babur.

An kama matashin ne bayan an masa ihu ɓarawo a kauyen Guru na jihar Bauchi a ranar 21 ga Nuwamba.

Bauchi
An kama barawon babur a Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook cewa matashin ya caka makami wa dan acaba a ƙeya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kwamandan 'yan ta'adda da wasu 114

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɓarawo ya sace babur a Bauchi

Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta bayyana cewa a ranar 21 ga Nuwamba ta samu kiran gaggawa kan a sace babur a ƙauyen Guru.

Lamarin ya faru ne bayan wani matashi da ake zargi ya cakawa dan acaba wuƙa a ƙeya ya gudu masa da babur kirar Bajaj.

Biyo bayan sace babur ɗin, ɓarawon da ake zargi mai suna Abdulrashid Abubakar ya nufi hanyar Jos domin guduwa.

An kama barawon babur a Bauchi

Biyo bayan samun kiran gaggawa, jami'an yan sandan caji ofis na Guru suka nufi hanyar da barawon ya bi.

A dalilin haka, yan sandan suka samu nasarar cafke Abdulrashid Abubakar wanda ya kasance dan unguwar Bakin Kura ne a cikin Bauchi.

An kwato babur wajen ɓarawo a Bauchi

Yan sanda sun kwato babur kirar Bajaj a wajen Abdulrashid Abubakar kuma ya bayyana cewa yana sata ne tare da wani matashi mai suna Adamu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ajalin matashin lauya a jihar Benue

Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi ya yabawa jami'an yan sandan caji ofis na Guru bisa kokarin da suka yi.

An kama barawon babur a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da cafke gawurtaccen ɓarawo da a ake zargi ya shahara da satar babur.

Rahotanni sun nuna cewa an kama barawon mai suna Kabiru Abubakar yayin da ya sace babur a farfajiyar asibiti a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng