Za a Baza Haja, Kamfanoni Sama da 300 Za Su Halarci Baje Koli a Kano

Za a Baza Haja, Kamfanoni Sama da 300 Za Su Halarci Baje Koli a Kano

  • Ana sa ran Kano za ta cika makil da yan kasuwa yayin da za a fara bikin baje koli karo na 45 a ranar Asabar
  • Ana sa ran kamfanoni daga ciki da wajen Najeriya ne za su hallara a kasuwar domin baza hajarsu ga masu sha'awa
  • Kamfanonin sun hada da kasar India da na Nijar, yayin da aka tsara cewa kowa zai iya shiga baje kolin kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - A ranar Asabar ne za a bude kasuwar baje koli ta duniya a Kano, inda tuni kamfanoni su ka shirya halartar gagarumin taron.

Cibiyar bunkasa ciniki da masana'antu da ma'adinai da ayyukan gona a jihar (KACCIMA), ta bayyana cewa shirye-shirye sun kammala domin tabbatar da taro mai inganci.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa ba su dandara ba, za su sake jajubo kudurin kara wa'adin masu mulki

Jihar
Kasuwar baje koli za ta fara ci ranar Asabar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban cibiyar, Garba Imam ya fadi adadin kamfanonin da ake sa ran za su halarci baje kolin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanoni za su halarci baje kolin Kano

BBC Hausa ta ruwaito cewa akalla kamfanoni 300 ne aka da tabbacin za su halarci kasuwar baje koli da za a bude a ranar 23 Nuwamba, 2024 a Kano.

Shugaban KACCIMA, Garba Imam ya kara da cewa kamfanonin sun hada da na cikin Najeriya da kasashen waje kamar su India da Nijar.

Kano: An sassauta dokar shiga baje koli

Alhaji Garba Imam ya bayyanacewa za a iya shiga baje kolin kyauta domin ba jama'a damar shiga kasuwar ba tare da wata matsala ba.

Za a gudanar da baje kolin karo na 45 na kwanaki akalla 15, daga 23 Nuwamba, 2024 zuwa 7 Disamba, 2024 domin ba al'umma damar shiga kasuwar.

An samu hauhawar farashi a kasuwar Kano

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun ƙara lalata turken lantarki, sun sace kayayyaki

A wani labarin kun ji cewa farashin kayayyakin abinci ya tashi a wasu daga cikin kasuwannin jihar Kano jim kadan bayan kammala zanga zangar adawa da yunwa.

An samu rahoton cewa farashin wasu daga cikin kayan abinci ya hau ne saboda karancinsa, biyo bayan saye wasu daga cikin kayan masarufi saboda fargabar zanga zanga da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.