Buhari zai kaddamar da kasuwar bajekoli ta Duniya a jahar Kaduna

Buhari zai kaddamar da kasuwar bajekoli ta Duniya a jahar Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake kai ziyara jahar Kaduna a watan Maris domin kaddamar da kasuwar duniya ta jahar Kaduna karo na 40, kamar yadda shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu Kaduna, Dakta Muheeba F Dankaba ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Muheeba ta bayyana haka ne yayin wata ziyara da ta jagoranci sauran shuwagabannin cibiyar suka kai zuwa ofishin kamfanin jaridar Daily Trust a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Tabarbarewar ilimi a Najeriya: Kalli yadda wasu daliban Firamari suke daukan darasi

Buhari zai kaddamar da kasuwar bajekoli ta Duniya a jahar Kaduna
KADCCIMA
Asali: UGC

A jawabinta, Muheeba ta bayyana cewa sama da kamfanoni 70 daga ciki da wajen kasarnan sun kammala shirin cin wannan kasuwa da shugaba Buhari zai kaddamar da budewanta a ranar Asabar, 30 ga watan Maris.

Kasuwar zata fara ci ne daga ranar Juma’a 29 ga watan Maris, kuma za’a kwashe tsawon kwanaki goma ana hada hada a cikinta, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da taimakon gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai zasu bude kasuwar a ranar 30.

A cewar Muheeba, taken kasuwar ta bana shine hadin gwiwa tsakanin kamfanoni da bangaren noma don cigaban Najeriya, kuma an zabi wannan take ne domin taimaka ma gwamnati a kokarin da take yin a sake farfado da tattalin arzikin kasar, tare da neman masu zuba jari a harkar noma.

Haka zalika shugabar cibiyar tace daga cikin al’amuran da zasu gudana yayin bikin bude kasuwar bajakolin ta duniya, akwai kacici kacici da suka shirya ma daliban makarantun sakanadari daga jahohi 19 na Arewacin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng