'Akwai Yunwa': Tinubu Ya Magantu daga Brazil, ya ba Yan Kasa Satar Amsar Shirinsa
- Shugaba Bola Tinubu ya kwantarwa yan Najeriya hankali kan halin kunci da yunwa da ake ciki inda ya dauka musu alkawura
- Tinubu ya fadi haka a birnin Rio de Janeiro da ke Brazil inda ya tabbatar ya san akwai yunwa a kasa amma za a caba nan kusa
- Shugaban ya sha alwashin kawo karshen karancin abinci da kuma rikicin manoma da makiyaya da ke da matukar tasiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Rio de Janeiro, Brazil - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan halin kunci da yunwa da ake ciki a Najeriya.
Shugaban ya ce tabbas akwai yunwa a kasa amma kuma akwai haske a gaba saboda wasu tsare-tsare da yake dauka domin kawo karshen matsalolin.
Tinubu ya fadi hanyar kawo sauyi a Najeriya
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ta wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya fadi haka ne yayin taro a kasar Brazil inda ya ce akwai wasu hanyoyi da yake bi domin inganta Najeriya da kawo karshen matsalolin da take fuskanta.
Shugaban ya kuma fadi yadda yake kokarin shawo kan matsalolin ƙarancin abinci da kuma rigimar manoma da makiyaya.
Tinubu ya tabbatar akwai yunwa a Najeriya
"Muna kokarin mayar da halin kunci da ake ciki da rashin tabbas zuwa inganta tattalin arziki da damarmaki a cikinsu"
"Za mu yi duba zuwa matsalolin da muke da su a kasar domin kawo damarmaki da ke ciki."
"Samar da abinci yana da matukar muhimmanci, a yanzu da muke magana akwai yunwa amma akwai haske a gaba wanda kowa zai shaida a hakan."
- Bola Tinubu
Tinubu ta sake ciwo bashin makudan kudi
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta samu rancen $500m daga Bankin Duniya domin inganta ayyukan kamfanonin rarraba wuta (Discos).
Kudin zai tafi wajen gyara layukan wuta, kara karfin na'urori, da siyan mitoci don inganta rarraba wutar lantarki a kasar.
Kamfanin TCN ya bayyana yadda kudaden za su taimaki kamfanonin rarraba wutar da kuma daidaituwar wutar a fadin kasar.
Asali: Legit.ng